Jagoran juyin juya hali na kasar ran ya bayyana cewa dole ne a karfafa gwiar matasa da kuma saita tunaninsu domin su bayar da gudunmawa cikin al'umma.

Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bukaci a karawa matasan kasar karfin guiwa da kuma tunani idan ana son ci gaban kasar Iran.

Jagoran ya fadi haka ne a jiya Asabar a lokacinda yake ganawa da mawaka masu yabon iyalan gidan manzon Allah(s).

Jagoran ya kara da cewa karafafa matasa a tunani da kuma sanin abinda zasu yi nan gaba yana nan kamar yi wa al-ummar Iran riga kafi ne mai karfi.

Jagoran ya kara da cewa, koyawa matasa ilmin iyalan gidan manzon Allah(s) na da ga cikin hanyoyin karfafa tunaninsu, da kuma kaifin hankali. Wannan zai zama garkuwa da kuma riga kafi ne ga tunaninsu, banda hakan wannan zai sa su fuskantar abinda yake gabansu ba tare da tababa ba.

Daga karshe jagoran ya kammala da cewa, matasa su ne manyan gobe, su ne zasu rike wannan kasar nan gaba, don haka karfafasu a bangarori daban-daban ya na da matukar muhimmanci.