*Jam'an Tsaro sun afkama yan uwa yau Laraba a kaduna*

Yau Laraba 26/2/2020 yan uwa Almajiran Sayyed Zakzaky (H) na kaduna Sun fito muzaharan qara kira ga Gwamantin da ta Gaggauta sakin jagora sayyed zakzaky muzaharan wanda aka fara daga Gwamna road dake kan by pass da misalin karfe 6:00pm ana cikin gabatar da muzaharan anzo dai dai wajan Masallacin Dahiru Bauchi dake kan By pass bayan an tashi yan uwa Sun fara tafiya kawai sai ga Yansanda nan sunzo zuwan su ke da wiya suka fara harbi kan mai uwa da Wabi cikin ikon Allah da yardan shi yan uwa suka kora jahiliyan bayan sun kora su sai ga yan qato da gora Sun fito suna gaba da addina suna gaba yansanda suna bayan su suna harbi su kuma suna danno yan uwa cikin ikon Allah yan uwa suka danna su da yansanda daga baya suka qaro karfi suka danno yan uwa izuwa yanzu Sun harbi yan uwa da dama daga ciki akwai shahidi daya sannan Sun kama yan uwa da dama musamman sisters  

Ga wasu daga cikin hotunan da muka dauko muku a wajan 

Kaduna Press 
26/2/2020