Babbar jami'ar majalisar dinkin duniya mai hada rahotanni kan laifuka da cizarafin dan adam ta bayyana cewa, kisan Kasim Sulaimani ya saba wa doka.

Bisa ga wani rahoto da tashar BBC ta bayar, babbar jami’ar majalisar dinkin duniya mai harhada rahotanni kan cin zarafin dan adam da kuma taka dokokin kasa da kasa Agnes Callamard ta bayyana cewa, kisan Kasim Sulaimani da Amurka ta yi, ya sabawa dokoki na kasa da kasa.

Ta ce an yi amfani da jirgi maras matuki wajen kisansa a cikin wata kasa da yake ziyarta a hukumance, wanda hakan babban laifi ne a dokokin duniya.

Callamard ta bayyana hakan nea  cikin wata a hira a shirin Hard Talk na tashar talabijin ta BBC.

Ta ko shakka babu abin da Amurka ta yi ya sabawa doka, domin Amurka ta yi amfani da jirgin yaki a kan mutumin da yake bako ne a wata kasa, kuma ya shiga Iraki ne a matsayinsa na babban jami’i na wata kasa a hukumance