Gwamnatin kasar Jamus ta saki dan kasar Iran Ahmad Khalili da take tsare da shi bisa bukatar bukatar Amurka.

Tashar talabijin ta Presstv ta bayar da rahoton cewa, kafin haka dai gwamnatin kasar ta Jamus tana shirin mika Ahmad Khalil ga gwamnatin Amurka ne, domin fuskantar shari’a kan abin da ta kira saba wa takunkuman tattalin arzikin da Amurkan ta dora wa Iran da ya yi.

Amma tare da kokarin jami’an diflomasiyyar kasar Iran a kasar ta Jamus, gwamnatin Jamus ta sallame shi ya kuma dawo gida tare da ministan harkokin wajen kasar Muhamamd Jawad Zarif, wanda ya halrci taron kasa da kasa kan harkokin tsaro.

Gwamnatin Amurka dai ta sha kama mutanen kasar ta Iran tare da tsare su bisa irin wannan zargi, na abin da take kira saba wa takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar.