A yau asabat 29/2/2020. Ne a ka gudar da addu'ar uku na shaheed jawwad Aminu Leman, Wanda ya yi shahada a ranar 26/2/2020, laraba da ya gabata, sakamakon harin ta'addancin gamayyan jami'an yan sanda, da yan kato da gora, tare da hadin yan iskan gari.

Wakilin yan uwa na garin Kaduna malam Aliyu Tirmizi ne ya jagoranci gudarnar da addu'ar, bayan kammala saukar alqur'ani mai girma tare da addu'o'i, malam ya gabatar da jawabi bangaren yan uwa da bangaren masu afkar da kisa.

Malam ya ce su wannan kisa suna yi ne dan suka sun Sanya razani a zugatan mu, sai ya kara da cewa lallai dayyid Zakzaky bai boye mana ba, ya fadamana zaumu gamu da kisa dauri da tsangwama da ga mahukunta da sauran al'umma, amma haka hanyar take, ba ranar da kisa zai hana tabbatuwar addini a wannan kasar.

Sannan malam ya yi albishir ga su masu aukar da kisa da su sani lallai a kwai ranar biyan bashi, tabbas rayukan mu da jinanan al'umma da suke shekarwa, Allah ba zai bari ba ya tafi a banza ba, ko da mu bamu yi komai ba Allah zai yi wani abu. Allah a cikin Alkur'ani mai girma hana cewa: (man katala mumin mutuhamida fah jazahu jahannamah khadina fiha abadan). Duk waanda ya kashe mumini da gangan to sakamakon sa jahannama, tin a duniya an bashi tikitin wutar jahannama na har abada. Kaga ko ba a maka komai a nan gidan duniya ba, Allah ya fadamaka makomarka a lahira, balanta ma kuma Allah ya yi Alkaurin zai sallada sa shen Ku a kan sa she.

Malam ya kara da cewa Alhamdulillahi mu a Kaduna shada ya zama mana jiki, kuma kwanan nan zamu sanya musabaka na yawan shaheedai halkoki a cikin garin Kaduna, a ga halkar da tafi bawa sayyid Zakzaky shahedai tin daga ranar 12/12/2015. Dan haka mu'assasatus shuhada su cigaba da hada lissafi, mugani wace halka ce ta zo na days, sannan za a baiwa na daya da na biyu da na uku lanbar yabo. Duk da musan tikitin su na wajen Allah, amma zamu bada tikiti ramzi ga ita halkar.

Daga karshe malam ya yi kira da yan uwa na Kaduna da su cigaba da shiga abuja, da kuma muzaharorin da ake yi a nan Kaduna,

Karda kuma mutuwa ya bawa wani Dan uwa tsoro wallahi ba a bun da zai faru da kai sai a bun da Allah ya kaddara maka, Dan haka bai yuwa wata ni rai ya mutu sai da iziin Allah. Ko da a na ruwan harsashi kamar yadda a ke ruwan sama wallhai sai wasun mu sun rayu, sunyi addini.

Sannan malam yayi kira ga yan uwa da su kara neman kusanci ga Allah, musamman a wannan watan da muke ciki na Rajab ga sha'aban da Ramadan. Don shahada ba bisa hadari bane, duk wanda kaga yayi shahada to a kwai abun da ya yi, Allah ya yarda da shi, ko da ko bakagani a zahiri ba.

Muna rokon Allah ya amshi  shahadar wannan Dan uwa namu, mu ma Allah ya bamu irin tasa.

Wasallallahu Ala Muhammad...

KNPRSCD 07
Kaduna Press
29/2/2020.