Majalisar dattijan kasar Amurka ta amince da daftarin kudirin da ya hana Trump yin gaban kansa wajen kaddamar da duk wani harin soji kan Iran.

Anadulo ya bayar da rahoton cewa, Majalisar dattijan kasar Amurka ta amince da daftarin kudirin da aka gabatar mata da ke yi wa Trump dabaibayi kan duk wani hankoronsa na kaiwa kasar Iran harin soji.

‘Yan majalisar dattawa 55 ne suka amince da daftrain kudirin yayin da 45 kuma ba su amince da shi ba, amma majalisar ta amince kasantuwar wadanda suka amince da shi ne suka fi rinjaye.

Dan majalisar dattijai daga jam’iyyar Democrat Tim Kaine ne ya gabatar da daftarin kudirin, inda dukkanin ‘yan jam’iyyar democrat da ke majalisar dattijai suka amince da shi, gami da wasu sanatoci takwas daga jam’iyyar Republican.

Tun a ranar Laraba da ta gabata ce dai Trump ya gargadi ‘yan majalisar dattawan da kada su kuskura su amince da wannan daftarin kudiri, inda ake hasashen cewa Trump din zai hau kujerar naki dangane daftrain kudirin, bayan da majalisar dattawan kasar ta Amurka ta yi watsi da bukatarsa.