A jiya ne aka saka wani babban mutumin mutumin Shahid Kasim Sulaimani a kudancin kasar Lebanon a kan iyaka da faasinu da yahudawa suka mamaye.

Rahotanni daga kudancin kasar Lebanon sun ce, an saka wani babban mutumin mutumin Shahid Kasim a kan iyaka da faasinu da yahudawa suka mamaye da kuma kasar ta Lebanon.

Wannan mutum-mutumi dai yana dauke da tutar Falastinu, kamar yadda kuma yahudawan da suke gadin iyakokin falastinu da suka mamaye suna kallonsa kai tsaye.

Ana ganin cewa sakon da hakan ke nuni da shi baya rasa nasaba da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar ne wajen fatattakar yahudawa a lokacin da suka mamaye kudancin kasar Lebanon, wanda hakan ke nuni da cewa al’ummar yankin suna sane da wannan gudunmawa.

Abu na biyu kuma al’ummar yankin suna kara tabbatar da cewa suna nan a kan tafarkin Kasim Sulaimani na fada da zalunci irin na ‘yan mulkin mallaka, tare da yin gwagwarmaya domin rayuwa a cikin ‘yanci.