-KADUNA PRESS.

A yau litinin 17/02/2020 ma 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy sun sake fitowa domin kara jaddada kiransu ga hukumomin Nigeria akan su gaggauta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy da mai dakinsa Malama Zeenat, daga tsarewar da suka kira ta haramcin da hukumomin ke yi musu tun a karshen shekara ta 2015.

Tsarewar tasu dai ta biyo bayan farmakin da jami'an sojin Nigeria suka kai masa a muhallinsa dake cikin unguwar gyallesu a cikin garin Zarian jihar kadunan Nigeria, bayan da suka kashe mabiyansa fiye da dubu 1000+, suka jikkata da dama daga cikinsu kana suka kame daruruwa daga ciki.

Muzaharar wadda 'yan uwan suka gudanar sun farata ne daga danmani junction, da misalin karfe 06:00pm na yamma, Kuma suka rufeta a kusa da masallacin Shehu Dahiru Bauchi, duk a kan titin Kaduna to Abuja Express way Kaduna.

Bayan kammala muzaharar ne dai jami'an tsaro sukazo bakin ruwa sunata harbe-harbe suna firgita al'ummar dake anguwa, sundaiyi harbin ne ta kasa da sama,

Izuwa hada wannan rahoton dai babu tabbacin cewa jami'an tsaron sunyiwa wani ko wata rauni ko kuma sun kama wani ko wata,
Sedai kawai cikin firgici ko zullumi da suka bar al'ummar yankin a ciki.
-J.S.A
-KNPRSCD 06.
-17022020.