Babban sakataren kungiyar Hizbullah akasar Lebanon ya bayyana cewa, duk da irin matsanatan takunkuman da aka kakaba wa Iran, amma ta tsaya a kan kafafunta.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar ko shakka babu al’ummomin yankin nan za su dau bindiga wajen yaƙar Amurka da sauran ma’abota girman kan da suka shigo yankin.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a yammacin jiya Lahadi wajen tunawa da zagayowar shekarar shahadar jagororin ƙungiyar da aka gudanar a birnin Beirut babban birnin kasar ta Labanon inda ya ce Amurka tana bin duk wata hanyar da ta sauwaƙa mata ciki kuwa har da kisan gilla don cimma manufarta ta mulkin mallaka a yankin Gabas ta tsakiya, don haka ya ce ko shakka babu al’ummomin yankin za su yaƙe ta.

Har ila yau kuma yayin da yake magana dangane da kisan gillan da Amurka ta yi wa Laftanar Janar Qasim Sulaimani, tsohon kwamandan rundunar Qudus ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran da kuma Abu Mahdi Al-Muhandis, tsohon mataimakin shugaban dakarun sa kai na ƙasar Iraƙi kuwa, Sayyid Nasrallah ya bayyana shahidan biyu a matsayin waɗanda suka taka gagarumar rawa wajen fada da ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh da kuma karya lagonta a ƙasar Iraƙin.

Don haka sai ya ce nauyin ɗaukar fansa jinin waɗannan manyan shahidan a matakin farko yana wuyan al’ummar Iraƙi ne, kamar yadda kuma ya ce ci gaba da kiyaye dakarun sa kai na ƙasar Iraƙin da ake kira da al-Hash al-Sha’abi wani nauyi ne da ke wuyan al’ummar ta Iraƙi.