-KADUNA PRESS.

A jiya asabar 01/02/2020 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy suka cigaba da gabatar da taron gasar Mauludin Sayyida Zahra a fadin Da'irar ta Kaduna da kewaye, a inda yau 'yan uwa na halkar Imam Mahdiy suka gabatar da nasu Maulud din.
Andai fara taron ne da misalin karfe hudu da wasu 'yan mintoci na yammacin wannan rana ta asabar.

Bude taro da addu'a keda wuya aka gabatar da karatun Alqur'ani, bayannan mawaka suka zo suka nuna tasu bajintar ta hanyar kure basirarsu suna sambado wakoki akan Sayyida Zahra, ba tare da bata lokaci ba aka tsallaka kan 'yan tamsiliyya, daga nan ne aka bukaci yara 'yan Fudiyya su yi fareti domin girmamawa ga Sayyida Zahra, daga nanne aka gabatar da ziyarar Sayyida Zahra, bayan haka ne aka gabatar da babban bako mai jawabi Sayyid Shareef Abdullahi Gamrash.
Shareef yayi jawabi mai tsawon gaske, ta yanda ya tabo dukkanin janibobi akan al'amarin daya shafi rayuwar Sayyida Zahra, kama daga haihuwarta, tasowarta, rayuwarta tare da mahaifinta, yanda ta kasamce bayan wafatinsa,
Sidi Gamrash yayi bayani gamsasshe a bisa rayuwarta da mai gidanta Imam Ali, kama daga yadda al'umma suka dinga gogoriyo wajen Ma'aiki da yanda Imam Ali yaje nashi neman auren nata,
A lokacin da Imam Ali ya zowa Ma'aiki saiyazo yanata jin kunya (da yake shi daman kunya a jininshi take) ya kasa fadawa Ma'aiki yanata inda-inda yana in-ina ya kasa magana sai Mai Tsira da Aminci yace masa ba Auren Sayyida ne kazo akanshi ba yace Ehh hakane sai Ma'aiki yace masa daman da kaine Allah ya umarce ni na kulla aure tsakaninku, haka nan aka dinga shirye-shiryen biki akayi aka kammala, inji malamin.
Bayan kammalawar shine aka bukaci wakilin 'yan uwa na Da'irar kaduna Sheikh Aliyu Tirmidhiy dayayi Ta'aliki a bisa jawabin da Malamin yayi,
Sheikh Tirmidhiy ya tabo abubuwan da ya kamata ya tabo ta ko wanne janibi,
Ba komaine mu zamu iya fadiba saboda muba 'yan gidan bane amman tunda 'yan gidan sun fadi shikenan, inji shi.
Duk abinda kaga anyiwa SHEIKH ZAKZAKIY to anyi masane saboda Ahli Baitin Ma'aiki karka-dada ko ka-raga wannan shine dalilin dayasa akayi masa dukkan abinda akayi masa.

Mun fara buga teburin alkali (WAI SUN KAWO SHEIKH ZAKZAKIY KADUNA IDAN ANYANKE MAI HUKUMCIN KISA ZASU ZARTAR) KANA NUFIN KA ZARTARWA DA JAGORA HUKUMCIN KISA KUMA KA CIGABA DA ZAMA LAMI-LAFIYA...?? AIKO WALLAHI TALLAHI BILLAHILLAZI DA ANYI ZARCE-ZARCE, DA AN ZARTAR DA ABUBUWA DA YAWA, DON WALLAHI BILLAHI BAZAKU ZAUNA LAFIYA BA.
Dan uwa da 'yar uwa kowa ya sanya kanbas dinsa ko kuma ya janyosu ya ajiye kusa dashi daga yaji ance a fito kawai ya fito,
Malam, Malama ko bacci zakayi dauko takalminka ajiyeshi kusa da kanka, ko kayi filo dashi ko ka daura abinka a kafarka domin kanaji ance a fito kawai ka fito.
Muna kara jaddada muku wallahi tallahi idan kuka kuskura kukayi abinda bai dace ba to zaku gani, inji Sheikh Tirmidhiy.
Bayan saukar Malamin daga munbari aka gayyaci Malaman su shiga cikin gurin da aka tanada domin nuna ramzin gonar fadak, bayan nan aka yanka alkaki, aka gabatar da kayan masarufi, akayi jawabin godiya aka rufe taron da addu'a aka sallami kowa.
-J.S.A
-KNPRSCD 06.
-02/02/2020.