Jami’an tsaron gwamnatin yahudawan Isra’ila sun hana musulmi gudanar da sallar asubahin yau a cikin masallacin quds.

Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, tun a daren jiya aka girke daruruwan ‘yan sandan yahudawa a sassa daban-daban na birnin Quds, da nufin hana musulmi halartar sallar asubahi.

Rahoton ya ce a lokacin da aka fara fitowa zuwa sallar da asubahin yau, yahudawan sun afkawa musulmi tare da hanasu shiga cikin masallacin quds, yayin da kuma wasu aka hana su zuwa masallacin.

Dubban musulmi ne suka gudanar salla a kan tituna da suke kusa da masallacin mai alfarma, kamar yadda kuma wadanda suka shiga cikin harabar masallacin, yahudawa sun lakada musu duka, tare da kame wasu daga cikinsu da kuma yin awon gaba da su.