YANZU-YANZU: Kotu ta saki tare da wanke dukkain 'Yan'uwa almajiran Shaikh Ibraheeem Zakzaky (H) 76 da suka rage a kurkukun Kaduna wadanda aka kama su aka garkame su tun bayan kisan kiyashin sojoji a Zariya a ranekun 12-15 ga watan Disamban 2015. 
Gwamnatin jihar Kaduna na ne a karkashin El-Rufai ta maka su a kotu tana zarginsu da aikata laifuka daban-daban ciki kuwa harda kisan kai. 

Bayan kwashe shekaru ana shari'ar, a yau Juma'a aka koma kotun domin yanme hukunci inda kotun ta wanke su tare da sallamar dukkanninsu. 

Idan baku manta ba, a dayan shari'ar ma da ta gudana irin wannan, kotun ta wanke tare da sakin 'yan'uwa 77, inda daga baya gwamnatin Kaduna ta daukaka kara, inda kotun daukaka karar suka tabbatar da hukuncin kotun farko. 


Cikakken rahoto na nan tafe daga baya. 


-AMR