Mutane da dama ne a Sudan suka gudanar da zanga-zaga domin neman a aiwatar da dukkanin manufofin juyin da suka yi.

Rahotanni daga Sudan sun ce dubban mutanen kasar sun gudanar da zanga-zaga a yau domin nuna neman a iawatar da dukkanin manufofin juyin da suka yi a cikin shekarar da ta gabata, inda suka daga tutocin kasar kuma suka nufi ofishin firayi inista.

Gungun kawancen jam'iyyun siyasa da kungiyoyi masu neman sauyi ne suka shirya gangamin, bisa abin da suka kira jan kafa da kuma kasa aiwatar da abin da al'umma ke bukata har yanzu.

Sabuwar gwamnatin kasar ta Sudan dai ta ce tana fuskantar matsaloli da dama wajen aiwatar da muhimman ayyukan da suke a gabanta, sakamakon matsaloli na tattalin arziki da kasar take a ciki.