Bankin Sterling daya daga cikin bankunan Najeriya ya bayyana shirinsa na yin aiki da tsari irin na muslunci ga masu bukata.

Shugaban bankin Sterling ya bayyana cewa, tuni suka fara aiwatar da irin wannan tsari ga masu bukata, kuma ya samu karbuwa matuka daga masu sha’aar hakan, yayin da kuam sauran harkokin banki suke tafiya kamar yadda suke bisa tsarin da aka saba.

Bashir Oshidi daya daga cikin manyan daraktocin bankin sterling ya bayyana cewa, bisa la’akari da bukatar da wasu adadi mai yawa na mutanen Najeriya suke da ita na son mu’amala ta banki ba tare da riba ba, wannan yasa suka dauki wannan mataki.

Kuma a cewarsa mutane da dama sun gamsu da hakan, inda hada-hadar banki ta karu matuka tun bayan bullo da wannan tsari ga masu bukata.