A daidai lokacin da 'yan Ta'adda suka gagari gwamnatin Jihar Katsina ta yanda suke cin karen su babu babbaka an zura masu ido.

Ranar jumaar data gabata ne 'Yan Ta'addan jami'an Tsaron Nigeria sukaje har gidan Wakilin yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky na Malumfashi Malam Kabir Imam suka  kamashi da 'ya'yanshi a yunkurin su wai na hana gabatar da Mauludin Sayyeda Zahra as wanda yan uwa zasu shirya a wannan rana. Bayan kama shi Wasu yan uwa sunje domin jin ba'asi suma suka kama su inda daga bisani suka saki yaran nashi su kuma suka tafi dasu katsina. 

Da safiyar ranar Asabar suka zo dashi har gida wai sunzo yin bincike ne, suka bincika babu abinda suka samu sai hotunan Sayyid Zakzaky guda bakwai da na Wasu daga cikin Shahidai  suka tattara suka tafi dasu. Katsam sai gashi yau sun kaisu kotu wai ana tuhumar su da Ta'addanci inda kotun ta turasu gidan Yari zuwa sai ranar 2/4 domin cigaba da Sharia. 

banda abin kunya irin na Jami'an tsaron Nigeria ga yan Ta'adda can suna Ta'addanci amma kun kasa kawo karshen sai bawan Allah da har makobta sun shaidi kyawawan dabiun shi, bashi da aikin da ya wuce neman ilimi da ilmantarwa tsawon rayuwar shi. A katsina akwai garin da yanzu haka ana hada kudi 1500 ko wane gida saboda yan Ta'adda sunce su aiko da kudin fansa ko su kawo masu hari amma jami'an Tsaron nan basuje sun kamasu ba. 

Malam Kabir satin da ya gabata aka sallamoshi daga asibiti yana kwance bashi da lafiya amma sun dauke shi babu kulawa balle magani sun kaishi gidan Yari. 

Allah kai hukunci tsakanin mu da wadannan azzalumai ka kawo mana karshen mulkin su na zalumci. 
Abban Mushfiqah 
25022020