Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Amurka ta saka wa Iran sabbin takunkuman tattalin arziki

A karkashin matakan murkushe Iran da Amurka ke yi, Amurkan ta saka takunkumi kan wasu kamfanunnuka 9 da mutane 3 da ke gudanar da aiyukan sarrafawa da hakar albarkatun man fetur a kasashen China, Hong Kong, Iran da Afirka ta Kudu.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar ta ce "Mun saka sunayen mutane 3 da kamfanoni 9 a jerin sunayen wadanda muka saka wa takunkumai saboda barazanar da suke yi na agazawa Iran ta bijire."

Sanarwar ta ce wadanda aka saka wa takunkumin suna da hannu wajen samar da kudi da taimakon 'yan ta'addar da suka kai hari da makaman roka a sansanin Taji da sojin Amurka suke zaune a Iraki, kuma wannan takunkumi na da manufar durkusar da Iran.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu