Sojoji 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin ta'addanci da aka kai wa sansaninsu a arewacin Mali.

Sanarwar da Rundunar Sojin Mali ta fitar ta shafinta na Twitter ta ce an kai harin ta'addanci kan sansanin soji dake garin Tarkint na yankin Gao a arewacin kasar.

An sanar da kashe sojoji 29 tare da jikkata wasu 5 a harin.

Tun shekarar 2012 ake samun hare-hare daga 'yan aware da 'yan ta'adda a yankunan tsakiya da arewacin Mali.