Yan uwa almajiran sayyid zakzaky na dandalin matasan halkan imam mahdi .
Dake dairan Kaduna sun gudanar da maulud na imam Ali.
Wanda daya daga cikin matasan halkan kuma mazlum wato TUKUR MUHAMMAD SULEIMAN. Wanda yafito daga makarantan annabi Yusuf. kurkuku .

Yayi jawabi mairasa zuciya sanan yajawo hankalin yan uwa matasa wajan koyi da rayuwa na imam Ali.
Sanan daga baya wakilin yan uwa MAL ALIYU TIRMIZI
.yayi taaliki mai tsawan gaske sanan ya jinjinama matasa wajan tsayawa kem akan tafarkin jagora
Sanan yayi nuni akan yanda matasa suke tsayawa suyi jawabi da kansu wajan bukukuwan maulud.
Hakan yana nuna cewa ansamu cigaba kenan koda wataran bamu muna da yakinin akwai Wanda insuka tashi suna bayani to dole ka gamsu .
Sabo da hikimomi da kuma gwarewa wajan yin maganan,sanan yayima sauran matasa na sauran yankuna dasuyi iyakan bakin kokarinsu wajan gabatar da bikin maulud dinsu kaman yanda aka tsara.

Daga baya kuma andaga
Manyan bana na hotunan
Shahidai matasa na halkan imam mahdi .
Wanda sune halkan da sukafi kowa yawan matasa shahidai a dairan Kaduna.
Sanan aka yanka alkaki .
Sai walima yabiyo baya

HOTUNAN
MAULUDIN NE KEBIYE MUKU A KASA


Kaduna press
KDPRSCD=005