,
Yau Alhamis5/3/2020 yan uwa Almajiran Sayyed zakzaky (H) na Dandalin Matasa na harkan Musulinci qarqashin Jagorancin Sayyed zakzaky na Darian kaduna suka fara Gabatar da Gasar Mauludin imam Ali(as) Wanda Halqar imam Hassan (as) suka Fara Gudanarwa taron wanda ya gudana a Kakuri dake Nasarawa Babban bako wanda ya gabatar da jawabi a wajan Shine Mal Alhassan Abdullah wanda yayi jawabi akan Jahadin imam Ali a rayuwar shi inda ya kawo tarihin shi da irin Gudunmawar da ya bayar a lokacin Manzon Allah (saw) daga karshe wakilin yan uwa na Kaduna Mal Aliyu Turmuzi kaduna ya gabatar da Ta'aliki daga qarshe yayi kira ga yan uwa Matasa dasu tashi tsaye wajan koyi da rayuwar imam Ali (as) Wajan ilimin shi da sadaukarwarsa daga qarshe aka yanka alkaki akai walima aka rufe taro da addua

Ga wasu daga cikin hotunan da muka dauko muku a Wajan

Kaduna press
5/3/2020
KNPRSCD 08
Safuwan Sp harun