A yau din nan ma Laraba 18/3/2019, dubbai 'yan'uwa na Kaduna da kewaye su fito muzaharar kiran a gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky, da mai dakinsa Malama Zeenatuddeen.

An tada Muzaharar ne da misalin karfe 6:00pm. na yamma a kan gwamna road dake kan titin Nmadi Azkwe bypass da ke nan cikin garin Kaduna.

An tafi da Muzaharar na tsawon wasu mitoci, cikin tsari da lumana a na ci gaba da kiran ga azzalumar gwamnatin Najeriya da ta gaggauta bin umarnin Kotu, domin sakin sa da mai dakinsa, kamar yadda Kotu tarayya ta wanke su daga dukkan wani laifi tun watan Disambar Shekara ta 2016.

In mai karatu bai manta ba, tun bayan harin ta'addanci gwamnatin Buhari, a shekar 12/12/2015, wannan azzalumar gwamnatin ke tsare da Shaikh Zakzaky, cikin rashin lafiya mai tsanani. Yau kimanin Shekaru biyar (5).

Tun a shakan 2016 babban Kotun tarayya dake Abuja ta wanke su, daga dukkan wani laifi ta kuma bada umar nin a sake su, amma gwamnati tayi kunnan uwar shegu da wannan umarnin, na kotu.

Da ga karshe dai An kulle Muz

aharar ne a Nan askolaye daura da Masallacin Sheikh Dahiru Bauchi a nan cikin garin Kaduna.