Sakon taya murna daga Kaduna Press

Wannan dan rubutun sadaukarwa ne ga dan uwan mu, abokin aikin mu, wato safwan (Sp) Harun, game da samun karu da yayi na ya mace, muna fatan Allah ya raya fatima.

HAIHUWA ITACE MUSABBABIN WANZUWAR RAYUWA

Danda mutum ya haifa  shine abinda zaisa a rika tunawa da mtutm bayan bashi, a zahirin al’amari danda zamu tafi mu bari shine zai zama gaado na hakika da zamu tafi mu barshi  a doron kasa , wanda zai zamo mai bauta ga ubangiji kuma mai nemar ma iyayensa gafara daga gareshi.

Da na gari, zai iya zama dalilinda zaisa iyayensa su zama abin yabo a bayan babu su, ya kuma zama sanadiyyar wanzuwar tunaninsu a zukatan al’umma .

Madalla da iyaye masu barin y’ay’aye irin wadannan da zasu zamo magadan halaye da kuma siffofiN iyayensu na gari .

     IMAM RIDHA (A.S) YACE :

“ duka wanda bai bar da  a duniya ba , kamar wanda baiyi rayuwa a cikin al’umma bane, amma wanda ya rasu yabar dansa a duniya kamar wanda yake rayuwa da al’umma ne (dukda cewa ya rasu)”

[1] Makarimul’akhlaq 219

[2] Musnadurridha 2/507