Isiya-Sy✍

Abul-Fadhal Abbas, daya ne da ga cikin ’ya’yan Imam Ali (AS), in ka ci re Imam Hasan da Imam Husain, a yayan Imam Ali, maza, to ba wanda ya kai shi daraja.

An haifi Abul-Fadhal Abbas a Madina, ranar 4 ga watan Sha’aban, shekara ta 26 bayan hijira.

Kuma Abul Fadhal Abbas tanadi ne na musamman da Imam Ali (AS) ya yi ma Imam Husain (AS) domin waki’ar Karbala.

Nasabarsa: Sunan mahaifiyarsa Fadima ’Yar Hizam.

Idan mutum ya bibiyi tarihinta, zai ga cewa baiwar Allah ce mai gayar biyayya da kuma girmamawa ga Ahlul baiti. Alal misali lokacin da ta zo gidan Imam Ali, wato bayan aurensu ta ce tana son idan Imam Ali zai kira ta, kada ya kirata da sunanta, wato Fatima, saboda girmamawa ga Sayyida Fadima, kuma kada haka ya dinga sosa ran su Imam Hasan, Imam Husain, da Zainab, wato saboda tunawa da Mahaifiyarsu.

To, a lokacin shi ne Imam Ali yake ce mata Ummu banin, domin daga baya ta haifi ’ya’ya maza guda hudu. Wannan kuma in muka duba za mu ga cewa wata karama ce daga cikin karamomin Imam Ali (AS). Haka nan kuma wadannan ’ya’ya nata ta yi masu kashedi da cewa, kada wani daga cikin su ta ji ya kira sunan Imam Hasan da Husain, sai dai su ce “Shugabana.” Kuma dukkan su wadannan ’ya’ya nata sun yi shahada ne a waki’ar Karbala.

Ga sunayen ’ya’yan nata da kuma shekarun da kowannensu ya yi a duniya:

Sayyid Abbas 34, 
Abdullah 25, 
Usman 21, 
Ja’afar 19.

Kuma dukkan wadannan ’ya’ya nata sun yi shahada ne a Karbala. Lokacin da labari ya zo Madina dangane da abubuwan da suka faru a Karbala, abin da ya damu Ummul Banin shi ne Imam Husain, domin wanda ya zo da maganar tana tambayar sa dangane da me ya samu Husain? Sai yake ce mata an kashe maki danki wane da wane.

Ta ce Husaini fa? Sai ya ce shi ma an kashe shi. Jin haka, sai ta fashe da kuka.

LAKUBBANSA
Sayyid Abul Abbas yana da lakubba masu yawa. Ana ce masa Kamaru Bani Hashim, wato saboda gayar kyan halitta da Allah ya yi masa. Ana kuma ce masa Babul-Hawa’ij, wato