Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

HAKIKANIN ABUN DA YA FARU A GIDAN KURKUKUN KADUNA YAU 31/3/2020....

Tun bayan bullar cutar Coronavirus (COVID-19), Kasashen duniya ke ta sakin yan gidan saboda kula da kiwon lafiya, akasin kasar mu NAJERIYA yayin da sukuma suke ta kara yawan yan gidan yari, ba wanda ya ce uffan, kwatsam sai a ka wayi gari wata daga cikin wadan da a ke tsare da su a gidan yarin bangaren mata, ta tashi da zazzabi mai tsanani sannan tana ta tari, wanda ake zargin cewa alamu ne na cutar Coronavirus, hakan ne ya sa hankali fursunonin gidan yarin hankalin su ya tashi sosai.

In suka ce ba su yarda da ciga ba da zama a haka ba, suna Kira ga gwamnati da a dau mataki, ba za su anmince da ciga ba zama a irin wanna halin ba, dole gwamnati ta daina kawo musu baki cikin su a cikin wannan yanayin, sannan suka ce dole ne su ma ma'aikatan Kurkukun su zauna a cikin gidan Kurkukun ba tare da fita ko zuwa ko ina ba, suna dawowa ba, tunda kowa a killace yake a gari saboda gudun yaduwar cutar Coronavirus (COVID-19) a cikin su.

Wanda hakan dama hakki ne a kan gwamnati ta kare lafiyar wanda da take tsare da su, amma sai suka Ki kulawa da wannan muradin na su da suka kawo, haka ne ya sa suka fara yekuwar cewa ba su aminta ba a sake su ko a kare lafiyar su. Nan abu ya yayi tsamari aka fara doke-doke tsakanin wadanda ake tsare da su da masu kula da gidan yari. Nan take aka turo sojoji inda suka fara harbe-harbe a harabar gidan yarin da kuma harba tiyagas daga yan sanda sunan wai ana yunkurin yin bore a gidan.

Sannin kowa ne jagoran Harka Musulunci a Najeriya Sheikh Ibarahim Zakzaky yana cikin wannan gidan kurkukun na Kaduna, kuma yana fama da rashin lafiya mai tsanani, sannan an zo a na harba tiyagas a cikin gidan, bamu da aminci da wadan nan mahukuntan, sabo da ba Allah a ran su, suna iya anfani da wannan damar su yi wani abu da ban.

Dan Haka muke kara kira ga wannan gwamnatin da ta gaggauta sakin jagoran Harka Musulunci da mai da mai dakin sa, kamar yadda kotun koli da ke abuja ta yi umarni a shekar 2016.

Muna kira ga Yan uwa da su kara daure damara, a cigaba da addu'o'i da ibadoji, Allah ya bawa Sayyid Zakzaky da Mai dakin sa lafiyar, ya kubutar da su daga hannun Azzalumai.

Sanarwa Daga Dandalin yada labarai na Harkar Musulunci A Najeriya Shiyar Kaduna.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu