A Najeriya, lauyoyin tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sunusi na II, sun fitar da wata sanarwa dake cewa, tsigewar da gwamnatin Kano ta yi masa ta sabawa doka.

Lauyoyin sun kalubalanci matakin da gwamnatin jihar ta dauka na tsige sarkin, inda suka ce majalisar zartarwar jihar ba ta da hurumin tsige sarkin, idan akayi la’akari da dokar kafa masarautu ta jihar Kano.

A cewar lauyoyin dokar ba ta ba gwamna ko kuma majalisar zartarwar jihar hurumin tsige sarki ba.

A ranar litinin ne dai gwamnatin Kano ta tsige Sarki Sunusi bayan tuhumarsa da rashin mutunta gwamnatin jihar, da wulakanta al’adun al’umma da kuma masarautar da yake jagoranta, zargin da a can baya ya sha musantawa.