‘Yan majalisar dokokin Amurka sun gabatar da bukatar janye haramcin bayyana masu hannu a kisan Khashoggi.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin Amurka, suna bukatar ganin an janye haramcin da aka sanya kan bayyana rahoton kisan Jamal Khashoggi, da nufin yin rufa-rufa kan wadanda suke da hannu kai tsaye wajen kisan nasa.

Dan majalisar dattijan Amurka daga jam’iyyar Democrat Ron Wyden, ya bayyana cewa, bisa ga dokar shekara ta 1976, kwamitin binciken bayanan sirri na majalisa yana da hakkin sanin hakikanin abin day a faru dangane da kashe Jamal Khasoggi.

Ya ce boye gaskiya kan hakikanin wadanda suka kashe Jamal Khashoggi da gwamnatin Amurka take yi, yana a matsayin halasta irin wannan mummunan aiki ne a nan gaba.

Idan kwamitin binciken bayanan sirri na majalisar dokokin Amurka ya amince da hakan, shugaban Amurka Donald Trump yana da kwanaki biyar a gabansa domin bayyana matsayinsa.

Tun abyan kisan gillar da jami’an tsaron Saudiyya suka yi wa Jamal Khashoggi a cikin ofishin jakadancin kasar da ke Istanbul a 2018, majalisar dokokin Amurka ta bukaci daraktan hukumar liken asiri ta Amurka CIA da ya bayyana mata sakamakon binciken da hukumar ta gudanar kan wadanda suke da hannu wajen Khashoggi, amma ya ki yin bayani, bisa hujjar cewa hakan zai cutar da tsaron Amurka.