A  ranar laraban da ya gabata ne aka cika shekaru biyar da Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan al’ummar kasar Yemen.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabi a daren shekaran jiya wanda gidajen talabijin na Yemen suka watsa kai tsaye daga birnin san’a, shugaban majalisar koli ta zartarwa a kasar Yemen Mahdi Almushat ya bayyana cewa, wanann rana ce ta kara azama da neman rayuwa cikin ‘yanci ga dukkanin al’ummar kasar Yemen.

Ya ce wannan rana tana a matsayin ranar kasa, domin kuwa ita ce ranar da al’ummar Yemen sojoji da sauran dakarun sa kai suka fara yaki gadan-gadan domin kare kasar daga wata sabuwar mamaya ta mulkin mallaka karkashin jagorancin Saudiyya, tare da taimakon wasu manyan kasahen yammacin turai.

Almushat ya ci gaba da cewa, tsayin daka da al’ummar Yemen suka yin a tsawon shekaru biyar a gaban ‘yan mamaya, ya tabbatar da cewa, har kullum masu gwagwarmayar neman ‘yancin al’ummarsu ba za a iya karya su ta hanyar luguden bama-bamai da killace su da yi musu kisan gilla ba, domin kuwa neman rayuwa cikin ‘yanci akida ce da ke cikin zuciya wadda ba za a iya rusa ta ba, ko da kuwa an kashe ma’abucin zuciyar.

Tun bayan da Saudiyya ta fara jagorantar kaddamar da hare-hare kan kan al’ummar kasar Yemen da sunan maida shugaban kasar mai ritaya Hadi Abdu Rabbuhu Mansur, ya zuwa yanzu a cikin shekaru biyar ta kashe dubban mutane, akasarinsu mata da kananan yara, tare da rusa daruruwan masallatai da cibiyoyin kiwon lafiya da na ilimi, da cibiyoyin kasuwanci, da dubban gidajen jama’a. tare da jefa rayuwar miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali.