.

A yau juma'a 06/03/2020 ma 'yan uwa musulmi sun sake fitowa domin kara jaddada kiransu ga hukumomin Nigeria akan su gagga
uta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy da mai dakinsa Malama Zeenat, daga tsarewar haramcin da hukumomin ke yi musu tun a karshen shekara ta 2015.Tsarewar tasu dai ta biyo bayan farmakin da jami'an sojojin Nigeria suka kai masa a muhallinsa dake cikin unguwar gyallesu a cikin garin Zarian jihar kadunan Nigeria, bayan da suka kashe mabiyansa fiye da dubu 1000+, suka jikkata da dama daga cikinsu kana suka kame daruruwa daga ciki.

Muzaharar wadda 'yan uwan suka gudanar sun farata ne daga kano road by Ahmadu bello way, da misalin karfe 06:00pm na yamma, Kuma suka
rufeta a mangal plaza junction.

Andai fara kuma ankammala lami-lafiya.
Kaduna press
-KNPRSCD 08