A Najeriya, ana zaman zullumi a yankin Naraguta da ke karamar hukumar Jos ta Arewa sakamakon aikin rusa gidajen jama'a da gwamnati ta fara yi a ranar Asabar.

Mazauna Naragutan sun ce sun wayi gari ba zato ba tsammani suka ga ma'aikata da jami'an tsaro wadanda suka hada da sojoji da 'yan sanda sun zo da manyan motocin gingimari, suka fara rusa gidajen jama'a.

A cewar mazauna yankin, wasu daga cikin wadanda abin ya shafa suna zaune a cikin gidajen aka fara rusawa ba tare da sun kwashi kayayyakinsu ba.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, Malam Sadisu Muhammad Musa ya ce tun bayan rasuwar mahaifinsa, bai taba shiga tashin hankali irin wannan ba a rayuwarsa. Ya ce ''an rusa mun gidana, an rusa mani komai''.

Wasu bayanai na cewa takaddamar ta samo asali ne yayin da Jami'ar Jos ke yunkurin shata iyakokin fili da ta saya da


Sai dai wasu daga cikin mazauna garin na cewa lokacin da ta zo shata filin nata, jami'ar ta wuce iyaka inda ta kebe har da wuraren da gidajen mutane suke, tana cewa duka nata ne.

  saidai bamu samu jin ta bakin hukumomin Jami'ar Jos ba.

Hakazalika lambar wayar kwamishinan filaye na jihar Filato ba ta tafiya, yayin da shi kuma kwamishinan ayyuka na jihar, Mista Pam Botman ya ce a ba shi lokaci, a kira shi daga bisani, saboda ba ya cikin yanayin da zai iya magana da 'yan jarida.

Shi kuwa kakakin rundunar tsaro ta musamman da ke aikin kiyaye zaman lafiya a jihar, Manjo Ibrahim Shittu, bai amsa kiraye-kirayen waya ba.

A cikin 'yan kwanakin nan dai wannan matsala ta iyakar fili tsakanin al'umar Naraguta da Jami'ar Jos na haifar da yawan takun saka da zaman dardar inda ko a makon jiya mutum guda eya rasa ransa yayin wata jayayya tsakanin matasa da jami'an tsaro da ke rufa wa masu shata iyakar filin baya.


KNPRSCD 08
Safuwan Sp harun