Isiya Sy ✍

Imamin Shi'a Na Bakwai Yau ce ranar 25 ga watan Rajab, wacce ta yi
daidai da ranar shahadar Imam Musa al-Kazim (a.s), Imamin Shi'a na Bakwai.

Haruna Rashid dai ya bi hanyoyi daban-daban wajen cimma burinsa na kashe Imam Musa al-Kazim (a.s).

Da farko dai ya umarci Isa bn
Ja’afar gwamnan Basra da ya kashe shi amma sai ya nemi uzuri daga Rashid, inda ya yi umarnin da a daga shi daga gidan yarinsa da mika shi zuwa gidan yarin Fadhl bn al-Rabi’, shi ma dai halaye da haibar Imam (a.s) sun hana shi aikata abin da ake so ya yi na kashe shi (a.s).

Ganin haka sai Haruna Rashid ya dauke shi daga wajen da mika shi
ga Fadhl bn Yahya, shi ma dai ya ki yarda ya aikata abin da Haruna Rashid ya ke son ya aikata.

Wannan lamari ya sanya shi ya koma ga shugaban sojojinsa a Bagadada wato al-Sindi bn Shahak, wanda ya yi fice wajen rashin imani da zalunci.

A nan dai an sanya Imam cikin mawuyacin hali.

Wata rana Haruna Rashid yana tafiya a hanyarsa ta zuwa Sham, sai ya shawarci wani na kusa da shi, wato Yahya bn Khalid kan kashe Imam Musa al-Kazim (a.s), daga nan sai Yahya ya kama hanyar zuwa Bagadada don tsara yadda za a aikata wannan danyen aiki.

Ko da ya isa Bagadada sai ya tafi wajen al-Sindi don gabatar masa da tsarin da aka yi na kashe Imam (a.s), nan take kuwa ya amsa masa wannan bukata, inda ya sanya guba cikin abincin da Imam din zai ci.

Bayan da ya ci wannan abinci, Imam ya fahimci cewa akwai guba a ciki saboda yadda yake ji a jikinsa, haka dai ya ci gaba da zama cikin wannan hali har na tsawon kwanaki uku, inda ya yi shahada a rana ta uku a cikin wannan gidan yari wato ranar ashirin da biyar ga watan Rajab shekara ta 183 hijiriyya.

Mahukunta dai sun yi kokarin boye shahadar Imam (a.s) da tattaro shaidun karya da suke nuni da cewa ya mutu ne haka kawai ba tare da wani ya kashe shi ba, hakan kuwa ya biyo bayan irin shakkun da mutane suke da shi kan faruwar wannan lamari.

Duk da cewa mahukunta sun kashe Imam Kazim (a.s) to amma tasirin da yake da shi a zukatan al’umma bai ragu ba face sai ma dada karuwa yake yi, ganin haka sai da
gangan suka bar Imam a gidan yarin har na tsawon kwanaki uku, kana daga baya suka fito da shi suka ajiye shi a wani waje suna kiran mutane zuwa ga jana’izarsa, suna cewa:“Ku duba ku gani wannan shi ne Musa bn Ja’afar ya mutu”.

Amincin Allah ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi, ranar da ya yi shahada cikin gidan yarin zalunci da kuma ranar da za a tashe shi yana raye mai ba da shaida a gaban
Ubangiji Madaukakin Sarki.

Muna taya dukkanin muminai juyayin wannan rana.