Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da hannu a tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu.

Mai Magana da yawun shugaban kasar ne Garba Shehu ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa Buhari bai sanya bakinsa a cikin takaddamar da ke tsakanin sarki Sanusi da gwamnan Kano ba, saboda hakan batu ne na jihar Kano.

Ya ci gaba da cewa, dukkanin maganganun da ake yadawa a shafukan sada zumunta kan cewa Buhari yana da hannu kai tsaye a cikin dukkanin abin da ya faru, ba gaskiya ba ne, magana ce dai kawai ta siyasa.

Kamar yadda kuma Buhari ya yaba wa al’ummar jihar Kano kan yadda suka nuna dattako bayan tsige sarki Sanusi na biyu, ta yadda suka zauna lafiya ba tare da tayar da hankula ba.

A ranar Litinin ya ta gabata ne dai gwamnatin jihar Kano karkashin shugabancin Abdullahi Ganduje gwamnan jihar, ya tsige sarkin Kano sanusi na biyu, tare da dora Aminu Ado Bayero, dan tsohon sarkin kano marigayi Ado Bayero a kan sarautar ta Kano.

Tun kafin wannan lokacin dai Ganduje ya dauki matakai daban-daban da nufin karya lagon Sarki Sanusi na biyu, da hakan ya hada hard a kirkiro wasu sabbin masarautu guda hudu a jihar.

Da yammacin jiya 11/3/2020 ne gwamna Ganduje ya mika wa Aminu Ado Bayero takardar kama aiki a matsayin sabon sarkin kano, tare da karbar sandar girma.