Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sojojin Najeriya 100 Sun Mutu A Harin Boko Haram

A kalla sojojin kasar 100 ne suka rasa rayukansu a wani harin kwantan-bauna da aka kai musu a arewa maso gabashin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayar da rahoton cewa, wata majiyar soji ta shaida cewa sun samu hasara rayukan sojoji 70 a harin na ranar Litini wanda ya faru a lokacin da sojojin suke aikin sintiri a kusa da dajin Sambisa da ke shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Haka ma akwai rahotannin da ke cewa 'yan bindigar sun yi garkuwa da wasu sojoji yayin da aka garzaya da sauran da suka jikkata asibiti.

Saidai da ta ke tabbatar da lamarin ga masu aiko da rahotanni Hedikwatar tsaron kasar ta ce sojin ta 40 ne aka kashe a harin

Kawo yanzu ba a iya tantance harin na kungiyar Boko Haram ba ne ko kuma wata kungiya da ke kai hare hare a yankin.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu