Daraktan hukumar lafiya ta Duniya a nahiyar Turai, Hans Kluge, ya yi kira ga kasashen Turai su dauki managartan matakan dakile yaduwar cutar COVID-19.

Hans Kluge ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana bayan taro ta bidiyo da ya yi da jami'an lafiya na kasashen nahiyar 53 a jiya, inda ya jaddada bukatar shigar da jama'a cikin aikin kare yaduwar annobar.

Jami'in ya ce ya zuwa jiya 17 ga wata, kimanin mutane 180,000 ne suka kamu da cutar a fadin duniya, inda 1/3n su ke Turai, lamarin da ya sa cutar ta fi Kamari a nahiyar.

Ya ce duk da cewa an samu bazuwar cutar zuwa kasashe sama da 150, matakan da kasashe kamar Sin da Koriya ta kudu da Singapore suka dauka, sun nuna cewa za a iya kare yaduwar cutar da ceton rayuka, idan aka dauki matakai kamar na gaggauta gano masu harbuwa da cutar da bibiyar wadanda suka yi hulda da masu cutar da rage taron jama'a da shigar al'umma cikin aikin yaki da cutar.