-Sheikh Adamu Tsoho Jos

A wannan lokacin da muke ciki muna cikin marhalan Jarrabawa, jarrabawa babba ga dukkan wani dan harka islamiyya a wannan kasa da ma kasashen duniya, domin Malam da'awansa ba kawai ta tsaya a wannan kasa bane, ba'a Africa bane da'awace wacce take alamiyya ta Duniya. 

Don haka a irin wannan jarrabawa da bamu taba fuskantar shi ba, duk da yake anyi jarrabawa a baya daban-daban to amma wannan jarrabawa tazo da wani salo tazo da karfi fiye da sauran jarabawowin da suka gabata basu zo da wannan karfin ba.

Allah ya kan jarraba mabiya Malam ne amma wannan jarrabawa da tazo! Tazo ne da manufar kawar da Malam daga doron kasa da kawar da Harka daga doron kasa a aikace ne suka gabatar, sun dauki dukkan matakai ne da zasu kawar da Malam wanda kuma mun gani da matakai na kawar da Harka da matakai na kawar da Almajiran Malam munga abin da ya gudana a wakiya din nan. Darurukan Almajiran Malam Maza da Mata Manya da Kanana harda tsofaffi wadansu ma da ransu aka kona su da wuta, wasu kuma da ransu aka binne su.

 Tare da --Idishia Jos. 

#FreeZakzaky.