Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) ta sanar cewa, yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar fashewar bututun mai a yankin Abule Ado dake birnin Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya ya karu zuwa 17, sannan mutane 25 sun samu raunuka inda ake ci gaba da ba su kulawa a asibiti.

Shugaban hukumar LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya bukaci mazauna yankin Abule Ado da su yi watsi da labarun karya da ake yadawa game da fashewar bututun man wanda ya afku da safiyar ranar Lahadi.

Tun da farko hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta sanar cewa, mutane 15 ne suka mutu, kana gidaje sama da 70 sun lalace.

Ya ce an sake samun wasu kananan fashewa bayan babbar fashewa ta farko, kuma hukumomi sun dukufa wajen gano musabbabin da ya haddasa fashewar.

Mele Kyari, babban daraktan kamfanin mai na Najeriya (NNPC), ya jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su, kana ya jaddada cewa, za'a tabbatar an kawar da dukkan gine gine da aka yi ta saman bututan man na NNPC domin kare afkuwar hakan a nan gaba.