Rana ta Farko ta Watan Ramadan
Bismillah
Ya Allah Ka sanya azumina a cikinsa (watan ramalana) ya zamanto azumi (dominka), Haka nan kuma tsayuwa ta (don salla) ta zamanto tsayuwar masu tsayuwa, Kuma ta farkar da ni a cikinsa daga barcin gafalallu, Ka gafarta min, Ya Ubangijin talikai, Ka yi min afuwa, Ya Mai yafe wa masu laifi.

Rana ta Biyu ta Watan Ramadan
Bismillah
Ya Allah Ka kusantar da ni zuwa ga abin yardarka a cikin wannan wata, sannan kuma Ka nesantar da ni daga abin da ba Ka so da kuam fushinKa a cikinsa, Kuma Ka bani damar karanta ayoyinKa a cikinsa, da rahamarka, Ya Mai rahaman masu rahama.

Rana ta Uku Ta Watan Ramadan
Bismillah
Ya Allah, Ka arzurtani, a cikinsa, da hikima da kuma fadaka, kana kuma ka nesantar da ni, a cikinsa, daga wauta da rashin sanin ya kamata, Ka arzurta ni da rabo na daga dukkan alherorin da Ka saukar a cikinsa, da karimcinKa, Ya Mai yawan karimci.

Rana Ta Hudu ta Watan Ramadan
Bismillah
Ya Allah, Ka karfafani, a cikinsa, da karfin yi maka biyayya, Ka dandana min, a cikinsa, zakin ambatonka, Ka arzurtani, a cikinsa, da daman gode maka, da karimcinKa, Ka kiyaye ni, a cikinsa, da kiyayewanka da kuma suturcewanKa, Ya Mafi ganin masu gani.

Rana Ta Biyar Ta Watan Ramadan
Bismillah
Ya Allah, Ka sanya ni, a cikinsa, daga cikin masu gafara, Ka sanya ni, a cikinsa, daga cikin bayinKa salihai masu tsantsaini, Ka sanya ni, a cikinsa, daga ciin waliyanka makusanta, da tausasawanka, Ya Mai yawan rahama.