A yau Alhamis  2/4/2020 daruruwa yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, sun fitowa domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  Buhari da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa tsawon shekaru fiye da hudu ba tare da laifin komai ba.
Sheikh Zakzaky na tsare tun bayan harin Ta'addancin sojojin Najeriya karkashin gwamnatin Buhari ta yi a ranar 12/12/2015, da kaisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da kona yayar sa da ranta a gaban sa, suka tsare daliban sa daruruwa.
A shekarar 2016 babban Kotun dake Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi. Gwamnatin taki tayi kunnen uwar shegu da maganar.
 
Bayan duk wannan ta'addancin da gwamnatin buhari tayi, har yanzu a sun ta kokarin sai sun kashe shi ta hanyar ciyar da shi da shayar da guba. Ga Kuma ma tsanancin rashin lafiyar da yake fama da ita, da iyalin sa. A haka su dauko daga inda suke tsare da shi a Abuja suka dawo da shi kaduna karkashin Nasiru El rufa'i, su ka fa haramtaciyar kotu wai suna tuhumar sa da tunzura mabiyan sa kisan kai, yayin da a ka ja lokacin a na gudanar da haramtaciyar shari'a da nufin yanke masa hukuncin kisa, amma cikin ikon Allah kotu ta kara wanke almajiran sa daga zargin da a ke mu su na kisan kai. 

Wanda hakan na nuni da zargin da a kewa jagoran Harkan Musulunci Sheikh Ibarahim Zakzaky bai da bai da tushe bare makama. Dan haka ne muke kara kira da babbar murya zuga Al'ummar duniya da su fahimci girman zaluncin da a kawa Malam Zakzaky da Al'majiran sa. Sannan A sau Malam Zakzaky ba tare da wani sharadi ba.

 Muna Allah wadai da Ta'addancin gwamnatin Najeriya a kan malam Zakzaky, da Al'majiran sa.

Yanzu haka dai gwamnatin na cigaba da tsare Sheikh Zakzaky (H) a gidan kurku da ke nan garin Kaduna, tare da iyalansa, duniya na ta Kira da a sakeshi, amma wannan gwamnatin tana nuna halin ko in kula.

Muzaharar dai ta daga ne da misalin 6:00pm a dai dai Dan Mani Junction da ke kan titin Nmadi Azkwe bypass a garin kaduna, yayin da a kayi tafiya mai tsawo, a ka mike hanya har zuwa Askwalaye daura da Masallacin Sheikh Dahiru yayin da a ka ka she muzaharar a nan.

Allah ka fatan ta rayukan Munudai da fitowar Allama Sheikh Zakzaky, ya kuma nuna mana ranar da za a kori zalunci a wannan kasar.

Isiya Sy
Kaduna Press
2/4/2020