A yau Laraba 29 ga watan 4 Shekarar 2020 daruruwa yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, sun fitowa domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  NAJERIYA da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa tsawon shekaru biyar ba tare da laifin komai ba.
 
Sheikh Zakzaky na tsare tun bayan harin ta'addancin Sojojin Najeriya karkashin gwamnatin Buhari, bisa jagorancin Shugaban Sojojin Nageriya Yusuf Tukur Burtai a ranar 12/12/2015, da kaisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da kona yayar sa da ranta a gaban sa, suka tsare daliban sa daruruwa, wanda a yauzu kotu ta wanke su daga zargin da ake musu wanda sukace wai sheikh Zakzaky ne ke ingiza su, kuma wanna ne laifin sa.
A shekarar 2016 ma babban Kotun dake Abuja ta wanke shi daga wannan zargi na gwamnatin buhari, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi. A bashi diyya, a gina masa gida a duk inda yake bukata a fadin kasar, amma gwamnatin taki, tayi kunnen uwar shegu da wannan maganar. Tana cigaba da rike shi.
Bayan duk wannan ta'addancin da gwamnatin buhari tayi a kan sheik Zakzaky da almajiran sa, sun ta kokarin sai sun kashe shi ta hanyar ciyar da shi da shayar da guba. Ga Kuma ma tsanancin rashin lafiyar da yake fama da ita, da iyalin sa. A haka su dauko shi daga inda suke tsare da shi a Abuja suka dawo da shi kaduna karkashin Nasiru El rufa'i, su ka fa haramtaciyar kotu wai suna tuhumar sa da kisan kai, yayin da a ka ja lokacin a na gudanar da haramtaciyar shari'a da nufin gubar da suka ciyar da shi ya yi tasiri a jikin sa, sai dai Allah Ubagiji ya nuna musu ikon sa, na cewa: rai a hannun sa yake, babu wani rai da zai mutu sai wanda Allah ya kaddara.
Haka a ka dau dogo lokaci a gudanar da wannan shari'a, kotu ta ba da umarnin a fita da shi waje domin kulawa da lafiyarsa, yayin da gwamnatin NAJERIYA ta yi kutsen a can kasar Indiya tare da kawayenta na kasar waje, don ganin sun cike burinsu na ganin bayan sa. Hakan bai yu ba sai suka yan ke shawara dawo da shi gida Najeriya. Suka cigaba da tsare shi ba bisa ka'ida ba.
Yanzu haka dai Sheikh Zakzaky (H) yana gidan kurku a nan garin Kaduna, tare da iyalansa, ba tare da laifin komai ba, duniya na ta Kira da a sakeshi, amma wannan gwamnatin tana nuna halin ko in kula.

Muzaharar dai ta daga ne da misalin 11:00am a dai dai Shatale Talen liventis zuwa kano road by Lagos street Kaduna.