Gwamna Abdullahi Ganduje 27/04/2020
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafaa don yaki da cutar korona a kasar ya yi watsi da jihar Kano duk da maawuyacin halin da jihar ta shiga.

Wakilanmu sun tattauna da Gwamna Abdullahi Ganduje, inda ta tamabaye shi halin da ake ciki.

Ganduje: "Halin da ake ciki yanzu muna da babbar matsala, kuma zan iya cewa da kai halin ba shi da kyau kuma abin tsoro ne. Domin babban abin da aka dogara da shi wajen shawo kan wannan al'amari shi ne wato dakin da ake gwaji."

Gwamnan ya kara da cewa: "Wannan dakin gwaji yau kwana biyar ko shida ba ya aiki. Kayan ma da ake dauka a kai aAbuja, suma sun yi karanci. Kuma ba kaya ne da gwamnati za ta je ksuwa ta saya ba. Kuma wadanda aka dauki samfurin jininsu suna jira, basu san me ye matsayinsu ba."

Ya kuma ce, "Wannan matsala ta Presidential Task Force, shi kansa Darakta Janar ya zo nan Kano ya kwana, amma tun da ya tafi ba mu sake jin komai game da wannnan maganar ba. Kuma shi ma Minista ya san cewa wannnan dakin gwaji ba ya aiki."

Ya ce "Saboda haka akwai babbar matsala. Tun da abin nan ya fara muke cewa Kano muna bukatar fiye da wurin gwaji daya."

Idan mun fahince ka akwai matsala, cewa ba kwa samun kula ko tallafi daga cibioyoyin gwamnatin Tarayya danagene da yaki da cutar korona.

Ganduje: Ai gaskiya ba ma samun abin da ya kamata, tun da yake wadannn abubuwa da a hannunmu suke, ai duk yadda za a yi sai mun sa shi yayi daidai. Amma gaskiya ba ma samun taimako da ma hadin kai daga shi wannan Task Force na gwamnatin Tarayya."

Farfesa Sadiq Isa Abubakar shugaban cibiyar yaki da cuttuka masu yaduwa na asibitin Malam Aminu Kano da jami'ar Bayero, dan kwamitin yaki da cutar korona a jihar ne.

"Halin da ake ciki hali na abin tsoro, bayan kwanaki da aka shafe ana yin gwaje-gwajen masu dauke da cutar korona, yanzu sai aka sami tsaiko."

Ya kara da cewa: "Jinkirin da ake samu kafin a fitar da sakamakon yana tsoratar da mu ma'aikatan lafiya".

Babban abinda ya fi daga hanakalin jama'a a yanayin da ake ciki na rashin sanin hakikanin illar da korona ke yi a jihar, da ma haske kan kiyasin mutanen dake dauke da cutar shi ne yawan mace-macen da ake samu a binin fiye da kowane lokaci a baya.

A cikin mako guda fitattun mutane da masu shekaru na kwanta dama a kusan dukkanin unguwannin jihar.

Cikin wadanda aka rasa daga Asabar zuwa Lahadi akwai farfesoshi guda hudu wanda na baya-bayannan shi ne Farfesa Balarabe Maikaba, na tsangayar nazarin aikin jarida a jami'ar Bayero dake Kano.

Abinda ke nan ya sa wasu masana harkar lafiya a wajen Kano ke nuna damuwa kan munin lamarin, kuma suke cewa da alama cutar korona ce ke wannan kisan mummuken.

Farfesa Usman Yusuf kwararren likita ne kuma tsohon shugaban inshorar lafiya na Najeirya.

"Duk inda ka ji wani dattijo ya mutu a ko ina a duniya - daga New York har Wuhan har Ghana - ko wace cuta ya ke da ita, yawanci za ka taras Covid-19 ce dalilin mutuwarsa."

Ya ce, "Irin wadannan dattijan da dama suna fama da wasu matsalolin rashin lafiya, kamar ciwon sikari, hawan jini da cutar huhu, irinsu ta ke zuwa ta daka ta tafi mana da su".

Yanayin da ake ciki dai a Kanon ya sa uwar jam'iyyar PDP ta kasa ta fitar da sanarwa tana mai cewa abinda ke faruwa a Kano abin takaici ne yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa daukar matakai na zahiri kan wannan batun mai tayar da hankali.

Daya daga jagororin PDP din a Kano Umar Haruna Dogowa ya ce a zahiri take cewa gwamnatin jihar ta gaza.

"Sauran jihohi kamar Legas da Ogun sun taka rawar gani kan yaki da wannan cutar, amma a jihar Kano babu wani abin a zo a gani da aka yi. Me yasa ba a samar da irin cibiyoyin bincike kamar yadda aka samar a wasu jihohin ba?"

Daya daya manyan abubuwan da suka fi daukar hankalin kan batun na Kano shi ne dakatar da gwajin cutar korona a cibiya daya tilo a Kano tsawon kwanaki.

To sai dai a yanzu a iya cewa matsalar ta kusa zuwa karshe, kamar yadda Dr. Isa Abubakar Aliyu daya daga cikin wadanda suke gwajin cutar ta korona a Kano ke cewa.

"Dama an kulle cibiyar ne domin a yi feshin magani. Feshin na daukar awa 48 kuma mun yi nasarar feshe ko ina."

Kaduna press

KNPRSCD 08

Safuwan Sp harun