Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Coronavirus ta kama mutum 101 a arewacin Najeriya rana ɗaya 30 Aprilu 2020Aika
Alkaluman hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya sun nuna a ranar Laraba 29 ga watan Afrilu cewa an samu adadi mafi yawa na mutanen da suka taba kamuwa da cutar korona a jihohin arewacin kasar rana guda.

Bayanan da ta fitar a wani sakon tiwita cikin dare, karfe 11:55 sun ce mutum 101 sun kamu da annobar a jihohi guda goma ciki har da babban birnin kasar Abuja.

Kano ce ke da kaso mafi yawa da mutum 24, sai Adamawa mai mutum 1 da Yobe wadda karon farko ke nan da samun bullar korona, ita ma mutum 1 ya kamu.

Alkaluman masu kamuwa da cutar na kara hauhawa cikin dan kankanin lokaci a jihohin Kano da Borno da Gombe da kuma Katsina.

Coronavirus: Gwamnatin tarayya ta yi watsi da Kano - Ganduje
An wayi gari da gawa yashe a gefen titi a Jihar Kano
Abba Kyari: Na yi rashin babban amini - Buhari
An fara samun bullar cutar ne a yankin arewa ranar Juma'a 20 ga watan Maris cikin Abuja, lokacin da Mohammed Atiku ya kamu bayan ya dawo daga wata tafiya zuwa kasashen waje.

Cikin kwana 40, alkaluman hukumar NCDC sun tabbatar cewa mutum 603 ne suka kamu da korona a jihohin arewa 19, har da Abuja birnin tarayya.

Kimanin kashi 40% na masu fama da annobar koronabairas a Najeriya.

Kogi ce kadai zuwa yanzu jihar da ba a samu bullar wannan cuta ba a yankin arewa.

A ranar Talata 24 ga watan Maris ne kuma aka bayyana bullar cutar cikin jihar farko a arewacin Najeriya, baya ga babban birnin Abuja, inda Gwamna Bala Mohammed ya kamu.

Haka zalika an sanar da mutum na farko da ya mutu a Najeriya sakamakon cutar ranar Litinin 23 ga Maris a Abuja, hukumar NCDC ta ce mamacin ya yi fama da su wasu kwantattun cutuka, kafin korona.

Iyalan Sulaiman A-Ci-Mugu sun ce ya rasu ne tun ranar Lahadi kafin sanar da batun ga jama'a washe gari.

Malam Abba Kyari kuma shi ne mutum mafi girman mukami a Najeriya da cutar ta halaka bayan shi ma an bayyana kamuwarsa a Abuja. Ya rasu ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu.

Daga Bauchi, an sake ba da sanarwar bullar korona jihar Binuwai ranar 28 ga watan Maris, sai kuma aka tabbatar da kamuwar Gwamna Nasir El-rufa'i na Kaduna duk dai a wannan rana ta Asabar.

Wani abin mamaki shi ne duk da yake, Binuwai ce jiha ta biyu da annobar ta bulla cikinta a arewacin Najeriya har yanzu mutum 1 ne ke da korona a jihar, cewar alkaluman NCDC.

Borno da Gombe na daga cikin jihohin da cutar ta shiga cikinsu a baya-bayan nan, amma kuma suna cikin wadanda cutar take saurin yaduwa a Najeriya.

Hukumar NCDC ta ce cutar ta kama mutum 64 a Gombe, yayin da 59 suka kamu a Borno.

Gwamnatin Najeriya dai ta aika wani ayarin likitoci zuwa Kano, inda ake fargabar cutar ta fi yaduwa a Najeriya baya ga Legas.

Jihar dai na fuskantar karuwar mace-macen da ba a tabbatar da sabubbansu ba a hukumance. Gwamnatin Kano wadda da farko ta musanta mace-macen, daga bisani ta ce suna da akala larurori irinsu zazzabin maleriya da hawan jini.

Cibiyar gwada samfurin cutar korona guda daya da ake da ita a jihar ta rufe tsawon kwanaki, kafin ta ci gaba da aiki ranar Talata 28 ga watan Afrilu.

Ana alakanta mutane da dama da suka kamu da cutar ta korona baya-bayan nan a wasu jihohin arewacin Najeriya da Kano.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce gwajin da aka yi wa wasu almajirai da jihar Kano ta mayar mata cikin 'yan kwanakin nan, ya nuna cewa biyar daga cikinsu na dauke da korona.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya ba da umarnin sake kulle Kano tsawon mako biyu a kokarin shawo kan bazuwar cutar korona da kuma dakile mace-,macen da ake samu.

Hukumar NCDC ta ce zuwa ranar 28 ga watan Afrilu, an yi nasarar kara yawan cibiyoyin gwajin cutar korona a yankin zuwa takwas a jihohin Kaduna da Borno da Kano da Sokoto da Filato da kuma Abuja.

Kaduna press

KNPRSCD 08

Safuwan Sp

Post a Comment

0 Comments

Close Menu