Labarin da Yake shigo mana Yanzu haka daga Majiya mai tushe Shine: Sanadiyyar Janye Jami'an Tsaro da Gwamnati tayi a wasu kauyukan zuwa Cikin Gari wai Saboda Hana Shige da ficen Jama'a Saboda Gujewar yaduwar Coronavirus, A Yanzu Haka Barayi ne Rike Da Muggan Makamai Suka Kori al'ummar Kauyen Dama Dake Karkashin Local Government din Sabon Birni A Jihar Sokoto Tareda Wawushe Dukiyoyinsu da Harbin Kan Mai Uwa da wabi.

Wanda hakan Yayi Sanadiyyar Salwantar Rayuwaka da dama a yayinda wasu kuma suka Tsallaka zuwa wasu kauyukan Nijar Domin Tsira da Rayukansu, sai dai har zuwa Yanzu babu wani Yunkuri da Gwamnati tayi domin Ceto rayuwar Wannan Al'ummar da a yake neman Salwantar da rayukan su, babu gaira babu dalili.          


- Anas Ibrahim arifeey *Kaduna press*
 KNPRSCD 11