Hakika watan Ramadam mai albarka yana da matukar muhimmanci a addinin Musulunci, kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: "Shi wata ne na Allah Madaukakin Sarki". Shi ne shugaban sauran watanni na Musulunci kuma wanda yafi su daukaka. Don kuwa kamar yadda muka sani a cikinsa ne aka wajabta wa dukkan baligi namiji da baliga mace mai hankali yin azumi, wanda yana daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci. A cikin wannan wata, mai azumi baya ga sauke nauyin da ya hau kansa na yin azumin, kuma ya kan sami wani kusanci na musamman da Ubangijinsa Madaukakin Sarki da kuma samun lada mai yawa wanda zai kasance masa guzuri gobe kiyama.

Lalle yana da kyau a san cewa falalolin da suke cikin wannan wata ba wai kawai sun takaita ga yin azumi ba ne, face dai duk wani aiki na alheri da mutum ya yi a wannan wata zai kasance masa babban lada kana kuma babban guzuri da kuma daukaka. A cikin wannan wata ne aka saukar da Alkur'ani mai girma, don haka ne yake da kyau a kan dukkan musulmi da ya karanta Alkur'ani da kuma fahimtar ma'anoninsa don fahimtar dimbin ilmi da hikiman da ke cikinsa. Don ta hakan ne mutum zai sami haske da kuma tsarkaka.

Watan Ramadam wata ne na azumi, yawaita salla, kyauta da dai dukkan sauran ayyuka na ibada. Musulmi ya kan azumci dukkannin wannan wata, sai dai kuma azumi na hakika, wato ya kiyaye cinsa da shansa, bugu da kari kuma kan harshensa idanuwa, kunne, tunani da dai dukkan wasu abubuwan da aikata su zai kai shi ga samun fushin Allah Ta'ala.

Wani abin kuma da yake da kyau musulmi ya kula da shi a cikin wannan wata shi ne yawan yin du'a'i, mika wuya ga Allah, neman gafara daga zunubbai da dai sauransu, don samun daukaka da kuma kulawa ta Ubangiji.

Baya ga haka kuma a cikin wannan wata akwai wani dare mai tarin albarka da alfarma wanda duk wanda ya riski wannan dare, to ya rabauta. Wannan dare kuwa shi ne Daren (Lailatul) Qadr, wanda yafi darare dubu (kamar yadda Allah Ya ce). Wannan dare kuwa ana samunsa ne a kwanaki goma na karshe. Wasu ruwayoyi sun ce ana samunsa ne a daya daga cikin wadannan darare, wato: daren 19 ko 21 ko kuma 23, duk da cewa wasu hadisan sun fi fifita daren 23 a kan sauran dararen.. A wannan dare, ana son mutum ya shagaltu da ibada da kuma neman gafara a wajen Allah Madaukakin Sarki.

Don haka muna fatan Allah Madaukakin Sarki ya sanyamu daga cikin wadanda za su rabauta cikin wannan wata mai alfarma kuma wadanda Zai 'yantar da su a cikin watan, amin.