Daraktan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin ta Najeriya, Charles Onunaiju, ya yi wani sharhi mai taken "Yadda tsarin duniya da al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam suke bayan yanayin tinkarar cutar COVID-19 " a wasu muhimman kafofin watsa labaru, ciki har da jaridar Blueprint da ta Peoples Daily da dai sauransu.

A cikin sharhin, ya ce cutar COVID-19 ta bulla ne a kasar Sin, amma ba ya nufin asalin cutar ya fito ne daga kasar Sin. Domin hana yaduwar cutar, kasar Sin ta tayar da jama'a tsaye, inda suka kaddamar da yakin tinkarar cutar, kuma ta samu babbar nasara, a waje guda kuma, an kafa katangar hana yaduwar cutar zuwa ketare. Ya zuwa yanzu, babu wanda ya kamu da cutar da ya fito daga kasar Sin a nahiyar Afirka, wannan ya nuna siffar wata babbar kasa dake sauke nauyin dake bisa wuyanta.

Baya ga haka, sharhin ya ce, shaidu sun tabbatar da cewa, yanzu kasashe daban daban na kasancewa al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam, yana mai cewa sai ta hanyar hada kai za a iya tinkarar kalubalen bai daya da bil Adama ke fuskanta a maimakon nuna kiyayya.

Sharhin ya ce, bisa kokarin da dukkan bil Adama suke yi, za a kawar da cutar a karshe, amma dole ne a yi tunani mai zurfi, kana babu wanda zai dakatar da ra'ayin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam. (Bilkisu)