LABARIN MUKHTAR DA GWAGWARMAYANSA A RAYUWA.
✒️✒️✒️✒️✒️
Bashir Kaduna✍️
Kaduna Press

Ina farawa da sunan Allah mai rahama maijin kai tsira da aminci su tabbata ga Annanbi Muhammad (S) da Iyalin gidan sa tsarkaka.

Yau muna tafemuku da wani labari mai ban tausayi dakuma darasi na rayuwa.

Wanda ni Bashir Kaduna Zan kawo muku musha karatu lfy.
⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️

Sunana mukhtar Ahmad Anhaifeni a katsina a wani kauye da akekira DABAI.
Nataso cikin kulawa na mahaifi na da mahaifiya duk da cewa ni dayane na miji a dakinta sanan mahaifin mu yana da mata uku. Mahaifiyata itace ta biyu Sanan Allah ya albarkaci gidan mu da yara munkai mu sha bakawai. Mahaifinmu yanada rufin asiri na kudi sosai da motocin noma sanan ya shara wajan noma duk fadin garin kowa yasan Alhaji Ahmad magajin gari.

Bayan tasowana a gidan na fuskanci kalubale masu yawa sakamakon yawan kulawa da mahaifiyata take bani a matsayina na danta daya kuma namiji.
Babana shima yana sona sosai .
Takai da baya iya zuwa wani waje Sai yatambaya ina mukhtar, tare muke zuwa massallacin juma'a, a motansa kiran Nisan sanan inzamu dawo ya tsaya a kanti yasayomin kayan tsaraba masu yawa ni da yan uwana, abokan babana duk sunsan ni.

Wata rana wani cikin abokan babana yace Alhaji Ahmad kabani mukhtar mana yazauna a gidana? Sai yayi murmushi yace alamarin wanan yaron na Allah ne inajin sa a raina, Kuma koda nabaka mukhtar kasan mahaifiyansa bazata bariba, Sabo da bata da wani yaro namiji, sai mukhtar.
 
A haka mukhtar yafara girma  yafara zuwa islamiya na gidan kwano makarantan baban yara. Mukhtar yana da kokari sosai, sanan mahaifinsa yayi mai alkawari in ya yi sauka zai sayama sa keke da kuma wasu kyauta masu yawa. Mukhtar yayita murna ya kara dagewa da karantu.

A gefe guda kuma mahaifiyan mukhtar tafara shiga tsana na abokan zaman ta, dama sauran makiya, duba da hallin da sukaga Alhaji Ahmad hankalinsa gaba daya yakoma kan karamin yaran gidan baki daya, sai suka addabeta sanan suka addabi mukhtar basu da wani aiki sai ganin suncutar da danta dakuma ita baki daya.

Allahu Akbar. Mahaifiyan mukhtar Aisha matace mai shuru shuru, Kuma mai hakuri matuka, Wata rana yayan mukhtar 
Wanda suke yan uba bayan sun dawo makaranta tayi ta kokarin dauko mukhtar zuwa tushen mangoro dasunan suyi wasa amma ita ba wasa bane a ranta. Burinta ta cutar da mukhtar kaman yanda suka tsara ita da mahaifiyar ta. Bayan tasamu nasaran riko masa hannu zuwa waje da nufin suyi wasa, Da zuwansu tushena mangoro basuyi mint uku ba sai kawai akaji Mukhtar ya tsandara kara Wanda yatashi hankalin kowa, mahaifiyar sa tana gidan tajiyo wanan sautin karan tafito a guje dan ganin mai ya same shi.

Dan sanin wani halli mukhtar yatsinci kansa kubiyoni Ni Bashir Kaduna
A rubutu na biyu.
🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽