Azzahra Badamasi Ishaq✍🏼
Kaduna Press
Cin abinci ko abin sha don yin Suhur yana da matukar muhimmanci da kuma lada mai yawa ga mai azumi.
Akwai ruwayoyi daban-daban da suke kira da yin suhur koda da ruwa ne kawai saboda muhimmancinsa.
Ga kadan daga cikin irin wadannan ruwayoyi da suke magana kan Suhur:
Manzon Allah (S) yana cewa: "Allah da ManzonSa suna salati ga masu neman gafara da masu yin suhur a lokacinsa. don haka ku yi Suhur koda da ruwa ne"
Manzon Allah ya ce: "Suhur albarka ne, don haka kada ku bar suhur koda kuwa da gutsuren dabino ne".
Haka nan kuma Imam Sadiq (a.s) ya ce Manzon Allah (s) ya ce: Ku yi Suhur koda da (kofin) ruwa ne, Lallai amincin Allah ya tabbata ga masu yin Suhur
0 Comments