Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

SAKON DA RUBUTU KE ISARWA A CIKIN AL'UMMA.....

✍️Daga Fatima Muhammad Ahamd Da Azzahara Badamasi Ishaq tare da Rabi'atu Sa'id Kaduna Press.

Kullum a na yawan fada mana cewa shi rubutu duk yadda aka yi shi yana da sakon da ya ke isarwa imma mai kyau ko akasin haka, marubutan kwarai kuma suna yin sa ne domin a ilimantar ko a fadakar ko kuma a yi hannunka mai sanda ga al’umma a kan wani bakon abu, ko wani abu da ya gallabi ko ya damu al’umma domin a samu sauki ko domin a gyara don ci gaban al’umma.

Tabbas mun tsinci kawunanmu a wani irin yanayi inda ake koke-koke kan lalacewar tarbiyya a tsakanin maza da mata; musamman ma yan uwa mu matasa. Har ta kai wasu bakin al’adu sun cudanya da al’adun Malam Bahaushe, an kori kunya da kawaici da sanin daraja da mutunci musamman a tsakanin mata wadanda suke dauke da tubalin gina al’umma.

Wayewar zamani ya sanya mace ta fito daga shingen kariya da darajar da addinin Musulunci ya yi mata, ta fito tana gogayya da maza a dukkan bangarorin rayuwa. Hakan ya sa mace ta shiga cikin kunci da gararin rayuwa a yau. 

Shakka babu matasa sune kashin bayan Al'umma, dan haka duk Al'ummar da ta rasa matasa na gari a cikin ta, to tabbas ana debe tsanmani da gagareta.

Wannan na daga cikin daliliai da ya sa mukayi zurfin tinani, mu bu de sabon babi dan ingata rayuwar matasan mu a yau.

Ku kasance da mu Fatima Muhammad Ahamd Da Azzahara Badamasi Ishaq tare da Rabi'atu Sa'id, a shafin Kaduna Press a filin mu na zuwa ga matasa, don fatakar ga yan uwa mu matasa, da sauran Al'umma.

Kaduna Press 20/04/2020

Dan Allah 🙏 ku taya mu yadawa dan kuyi tarayya damu wajen aikin alheri🌹

Post a Comment

0 Comments

Close Menu