Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sayyed Zakzaky Yayi Rabon Kayan Abinci Ga Mabuqata


Kamar kowace Shekara Duk Idan Watan Ramadan Yakama Sayyed Zakzaky Yana Bayar da Gudummawar Kayan Abinci Ga Mabuqatan Dake Cikin Unguwar Dayake Kwana Gyallesu da Wasu Unguwannin dake Cikin Garin Zaria .
Kafin Kisan Kiyashin Zaria 2015. Da Gwamnatin Buhari tayi akan yan uwa Musulmi na Harkar Musulumci a NAJERIYA Sayyed Zakzaky Ne yake Rabawa dakan sa, Amma Yanzu Sakamkon  Tserewar Zalumcin Da Gwamnatin Buhari take Masa Yanzu Sai dai ya Wakilansa Suke Rabawa a Madadinsa Kamar yadda yayi Masu Umarnin Da cewa Duk Abinda yakeyi Dakaa a Fasa .
A Shekarar Farko Bayan Kisan Kiyashin Zaria Ganin Irin Mummunan Dabi'u Da Mutanen Unguwar Suka Nuna Na Goyon Byan Wannan Zalumcin Da Buhari yayi Ma Sayyed Zakzaky , An Tambayi Sayyed zakzaky da cewa shin harda Wadannan Dasukayi ta Murna Da Nuna jin dadi a kan Wannnan Abinda akayi Maka ? cikin Abinda Sayyed zakzaky yake cewa Shine Sune Farkon Wadanda za'a Fara Bamawa .
Alhamdulillah Banama Sayyed Zakzaky ya Raba Wananna Kayan Abinci Ga Mabuqata Kamar Yanda ya Saba  tsawon Shekaru Batare Da Cire Wanda yayi Murna da Abinda Akayi Masa Na Zalumci ba Lallai Sayyed zakzaky Rahmane a Cikin Al'umma

Allah ya Gaggauta kubuto Mana Shi daga Hannun Azzalumai.

#FreeZakzaky
29/April/2020

Post a Comment

0 Comments

Close Menu