(Wannan shi ne maudu'in da aka gabatar a bikin Nisfu Sha'aban da aka yi a zauren Khairul Amal na WhatsApp).

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.

Tsira da Amincin Allah su  ci gaba da tabbata ga Manzon Allah da Iyalan Gidansa Tsarkaka.

Allah Ina rokon ka shiriya, da taimako, da dacewa cikin wannan aiki.

An ce in yi magana kan topic Mai kanu: GWAGWARMAYAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H).

KALMOMIN MAUDU'IN MU:

MA'ANAR GWAGWARMAYA:
Kalmar Gwagwarmaya a Hausa na nufin; Yin fama da wani abu, ko yin kokawa da tataburza da wani al'amari.

Wannan shi ne makamanciyar fassarar da Qamusun Hausa na jami'ar Bayero ta Kano a shafi na 180 ya yi wa kalmar Gwagwarmaya.

Ita wannan kalma ta Gwagwarmaya, ita ce a Larabci ake kira MUQAWAMA.

A harshen Turanci kuma, Gwagwarmaya ita ce STRUGGLE, wanda ma'anarsa ba ta boyu ga masu Qamusun Turanci ba.

A takaice, ma'anar Gwagwarmaya shi ne yin fama ko yin kokawa da wani abu a kokarin iy masa ko yin galaba a kansa.

MA'ANAR SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY.

Kalmar SHAIKH kalma ce ta Larabci, wacce ke jujjuyawa daga zamani zuwa zamani ta hanyar karbar ma'anar da mutanen zamuna ke bata.

Asalin kalmar Shaikh tana nufin tsoho ne mai yawan shekaru da furfura.

Daga baya sai ake amfani da ita akan shugabancin wata kabila ko jama'a, wato in an ce SHAIKH to ana nufin shugaban 'yan wata kabila, ko shugaban wasu jama'a.

Amma a wannan zamani,  kuma a duniyar musulmi, in an ce SHAIKH, to ana nufin malami masanin addini.

IBRAHEEM ZAKZAKY kuwa, suna ne na wani bawan Allah malamin addinin Musulunci, Wanda mutumin Nijeriya ne da aka haifa a wani lardi da ake kira Zazzau, cikin wani gari mai suna Zariya, a shekarar 1372 hijira, daidai da 1953 miladiyya.

Daga sunan lardin Zazzau ne ya gina laqabinsa na ALZAKZAKY.

Kenan Atakaice, maudu'inmu mai taken; GWAGWARMAYAR SHAIKH  IBRAHEEM ZAKZAKY, na nufin fadi-tashi da faman da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ke sha a tafarkin rayuwarsa ne a fagen addini.

FADIN MAUDU'IN MU:

Wannan maudu'i mai fadi ne fiye da kima, ba ma za mu iya sanin gwargwadon fadinsa ba, illa iyaka dai mu za mu caccanki iya abin da muke iya tsinta ne mu yi tsokaci akai.

Da yake maudu'in cewa yake Shaikh Zakzaky da Gwagwarmayarsa, kenan muna da damar kallon fanoni da yawa da Shaikh din ya yi Gwagwarmaya da su, ba lallai mu takaitu kan Gwagwarmayar Musulunci ba.

GWAGWARMAYARSA A FAGEN NEMAN ILIMI:

Gwagwarmayar neman ilimin addini ita ce gwagwarmayar farko da Shaikh Zakzaky (H) ya fara yi a tafarkin Rayuwarsa. Tun talatainin tasowarsa bai muhimmanta wani abu fiye da neman ilimi ba.

ILIMIN ADDINI:

A hirarsa da gidan Talabijin din "Pure Streem" ya fadi cewa; "Bayan tasowa ta dai na fara karatu a wajen mahaifina ne, kamar yadda na ce shi malamin Alkur'ani ne, kuma karatun Alkur'ani na karanta a wajen shi, abin da muke kira Babbaku da Farfaru sannan kuma da Tashiya (wato mikewar karatu).

"Sannan kuma duk da haka ya sa ni a makarantar Alkur'ani ta wani Malami daban, wanda yake akwai yara da yawan gaske da suke hadda a wajan.....

"Muna da wata ka'ida na cewa sai ka sauke Alkur'ani za ka fara karatun littattafai na zaure, saboda haka bayan na sauke din sai na fara karatun littattafan, tun kamar Ina dan shekara 14.

"Karatun littafai wanda dai ake yi a nan kasar daidai gwargwado na yi su, ta fuskacin Luga da Nahwu da Sarfu, lallai Nijeriya ba ta gaza sauran sassan duniya irin Misra da Iran da Iraki ba, duk kusan littattafai daya muke karantawa, kuma daidai gwargwado na karanta su tun daga kananan littattafai irin su Ajruma, Mulha, Saja'i, Alfiyyar dan Malik duk mun yi wadannan".

Sannan ta bangaren Luga  na karanta irin su Ishiriniyah, da Witriyyah, da Ashariya, da Maqamatul Hariri da Shu'ara'ul Jahiliyyah da sauransu.

A bangaren Fikihun Malikiyya duk littattafan da ake karantawa a karatun fikihun Malikiyya na karanta su har zuwa Mukhtasar.

ILIMIN ZAMANI:

Bayan gwagwarmayar karatun addini da Shaikh Zakzaky ya taso da ita, a gefe guda ya ribanya gwagwarmayar tasa zuwa ninki biyu, inda ya sake sabar neman ilimin zamani na Nizamiyya a lokaci guda.

Ya shiga makarantar Islamiyyah ta "Fada Provincial Arabic School' ya karanci Nahwu da Luga.

Sai makarantar koyar da harshen Larabci ta 'Madrasatu Ulumul Arabiyyah, Kano' wacce a turance ake Kira 'School of Arabic Studies', inda ya zurfafa karatun harshen Larabci da kuma darussan boko.

Daga nan ya tafi Jami'ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya, inda ya karanci ilimin tsimi da tanadi (Economic) a Jami'ar.

Baya ga wadannan karatuttuka masu manhaja, Shaikh Zakzaky ya yi karatun zaure a fannonin ilimi daban-daban a gaban fitattun malaman addini, irinsu Malam Sani A. Fateh, Malam Sani Na'ibi, Malam Isah na Kwarbai, Malam Ibrahim Nakakaki,  Malam Aminu na Madaka, Malam Nuhu limamin Yola, Malam Datti Ahmad, Shaikh Abdurra'uf Usman, Shaikh Isah Waziri da sauransu.

A bangaren ilimin addini fannin Ja'afariyya kuwa, har zuwa yau ba a iya kididdige malaman da Shaikh Zakzaky ya yi karatu a wurinsu ba, abin sani dai kawai shi ne ya yi kuma yana ci gaba da yin karatu a wuraren manya-manyan malaman Shi'a kwararru a fannoni daban-daban a kasar Ghana, Lebanon, da Iran.

A takaice, gwagwarmayar Shaikh Zakzaky a bangaren neman ilimi har yau ba ta tsaya ba, domin har aka yi waki'ar Zariya, bai fasa fita waje neman ilimi gun masana ba.

GWAGWARMAYA DA KASALA DA MUTUWAR ZUCIYA:

Daga cikin alamun nagartar yaro, akwai kwazo da hazaka ko kazar-kazar, ma'ana rashin kasala da son jiki yana daya daga cikin alamomi da ke nuna cewa an yi sa'ar haihuwar yaro.

Shaikh Zakzaky (H) tun yana karamin yaro, ya taso ne da fuskantar Gwagwarmayar rayuwa, sam bai taso da kasala da son jiki wanda ke haifarwa Dan Adam mutuwar zuciya ba.

Tun yana dan karami ainun yake raka mahaifinsa Gona, yakan je ya taya babansa aikin gona irin wanda zai iya, ya'alla cirar ciyawa ne, ko shuka, ko ma sharar gonar ne da sauransu.

A wata hirarsa da jiridar ALMIZAN yana cewa; "An haife Ni a garin Zariya, kuma har ya zuwa daidai lokacin da na soma wayau zuwa lokacin da na kai shekaru 17, rayuwata abu biyu ne kawai, zuwa makaranta da kuma zuwa Gona, gona dai wadda aka sani, mahaifina daman manomi ne, nakan je in taimaka Masa wajen aikin gona". (Tarihin Harkar Musulunci, 14).

KIWON DABBOBI:

Ba kawai hidimar noma Shaikh ya taso da ita a lokacin yarintarsa ba, a'a, a gefe guda yana kiwon tumaki da awaki na gidansu, dama dai an san rayuwar Hausawa magabata ba sa rabuwa da kiwon kananan dabbobi a cikin gida, dan haka Shaikh Zakzaky yakan raka wadannan dabbobi zuwa kiwo a daji.

A wata laccarsa lokacin wani bikin zagayowar ranar haihuwarsa ya ce; Na taso ne a gidan mu da zuwa noma da kiwo ba ya ga karatuttukan addini da muke yi".

Wannan Gwagwarmaya ta noma da kiwo da Shaikh Zakzaky ya taso da ita ta zamo jiki gare shi, ta yadda duk da girma da daukakar da Allah ya yi masa, amma bai daina noma da kiwo ba, duk shekara yana noma, yana da tafka-tafkan gonaki a yankin Zariya da yake noman abubuwa daban-daban.

Haka nan a bangaren kiwo ma har waki'ar Zariya 2015 bai taba wofinta daga kiwo ba, hasali ma ita kanta waki'ar ta rutsa da wasu manya-manyan dabbobinsa irin dawaki, shanu, talo-talo da sauran dabbobin da yake kiwatawa a Darur Rahma da ke bayan garin Zariya.

KASUWANCI:

Tabbataccen abu ne cewa Shaikh Zakzaky (H) ma'abocin sana'a ne ko kasuwanci, yana da nau'o'in kasuwancin da yake gudanarwa ta hanyoyin wasu da ya dora akan hidimar, wasu kai tsaye, wasu kuma a fakaice.

A gefe guda, makusanta sun ruwaito cewa Shaikh din yana kasuwanci na sanya hannun jari a kamfanonin 'Halal Bussinesis', wato kasuwancin zamani da mutum ke yinsa yana zaune a gida ta hanyar na'urorin zamani.

A takaice, wannan tsokaci yana nuna mana cewa Shaikh Zakzaky (H) bai yi zaman dirsham da tsammanin warabbuka a wurin kowa ba a duk tsawon rayuwarsa, ya tashi ne da gwargwarmayar neman na kansa, Wanda wannan bangare ne na kamalar Dan Adam.

A nan, mu da 'ya'yan mu muna da abin koyi, cewa Gwagwarmayar dogaro da kai, daya ce daga muhimman gwagwarmayoyi na kamalar mutum da mutumtakarsa.

AYYUKAN DOGARO DA KAI:

Daga cikin Gwagwarmayar dogaro da kai da Shaikh Zakzaky (H) ya sha a tafarkin rayuwarsa akwai yin wasu ayyuka da yake da masaniya game da su don samun halaliyarsa.

Misali, a lokacin da yana matashi dan shekaru tsakanin 15 zuwa 20, ya yi ta sintirin koyarwa a makarantun Islamiyyah daban-daban.

A wata Hira da shi ya ambaci cewa, a lokaci guda yana karantarwa a makaratu hudu daban-daban a cikin birnin Zariya, daya a unguwar Kwarbai, daya a unguwar Kakaki, daya a unguwar Lemu, daya a unguwar Rimin Tsiwa duk a cikin birnin Zariya.

Duk wadannan makarantu yakan je ya koyar a cikinsu lokuta daban-daban a rana guda, kuma ga karatunsa da yake yi na zauruka da na Nizamiyya duk a lokacin.

Ko ba mu fada ba, wannan a zahiri Gwagwarmaya ce ta bada ilimi da kuma bin hanyar dogaro da kai don wadatuwa da halal.

GWAGWARMAYA DA ZUCIYA DA SHEDAN:

Allah Ta'ala yana fadi cikin Alkur'ani cewa; (Shi Dan Adam) Mun shiryar da shi tafarki biyu, ko ya zama mai Godiya, ko kuma ya zama mai kafircewa".

A yayin da mutum ya zabi ya zama mai Godiya (wato mai bin Allah Ta'ala), to tabbas ya ballowa kansa Gwagwarmaya mai zafin gaske da rundunoni biyu na makiya, rundunar son zuciya 'Hawa' (wacce Allah ya bayyanata da cewa; Abin sani ita zuciya mai umarni ce da mummuna), da kuma rundunar Shedan da tawagarsa, wanda ya rantse cewa ba zai bar kowa ya bi Allah sai wanda ya fi karfinsa.

Gwagwarmaya Shaikh Zakzaky da wadannan rundunoni abu ne mai ban mamaki da ban Sha'awa kwarai.

AIKIN HAJJI:

Ba boyayyen abu ne ga duk wanda ya san rayuwar Shaikh Zakzaky (H) ba, cewa tun cikin shekarun tamanoni (80s) Shaikh din ke zuwa aikin Hajji da yawan zuwa Umrah babu kakkautawa har zuwa shekarar 1995.

A Gwagwarmayar bautawa Allah a wurare masu tsarki na Makkah da Madina, Shaikh Zakzaky a shekarun baya yakan tafi Umrah ne tun a karshen watan Jimada Thani, wato daya ga watan Rajab takan same shi ne a Ka'aba, inda yake dukufa ibada a jikin 'Muqamu Ibraheem' har sai bayan karamar Sallah yake dawowa gida Nijeriya. Duk shekara haka yake yi, har sai da kafircin duniya karkashin wakilcin Saudiyya suka matsa kaimin sa shi a 'Target' sannan ya canza taku.

Zuwa yanzu babu takamemiyar kididddiga da ta fayyace sau nawa Shaikh Zakzaky ya yi Ummrah da aikin Hajji a rayuwarsa.

SALLAR NAFILA:

Linzami ya fi karfin bakin Kaza in aka ce za a yi magana akan Gwagwarmayar sallolin nafilfili na neman kusanci ga Allah da Shaikh Zakzaky ke yi a tafarkin rayuwarsa.

Ya ishe mu fahimta in muka ce, Shaikh yana yin dukkan nafilfilin da ake son yi kafin da bayan sallar farilla, sallolin Tahajjud da na darare masu alfarma, sallolin yininnuka da na ranakun kowane wata, sallolin musamman a darare masu alfarma, sallolin watannin Rajab, Sha'aban da Ramadan, da ma duk wata Sallah da aka ruwaito son yinta a lokaci na musamman.

Marubucin littafin 'Malam Malam ne' yana cewa; "In ma Malam yana barci a dare, to fa kadan ne! Sau da dama za ka ji yana cewa, "Rabona da bacci tun kwana kaza!".

A wani jawabi da Shaikh Zakzaky ya yi wa wasu da suka kawo masa Ziyara a wani watan Sha'aban, ya ce; Da za a tambaye Ni me ka fi so? Zan ce Sallah! Da za a ce mun me ka fi jin dadinsa? Zan ce Sallah!" (Shaikh Zakzaky Ikon Allah, 108).

A wani jawabinsa na karfafa almajiransa ga ibada da sallar dare yana cewa; "Dare yakan yi mun kadan, da da yiwuwar a kara da na so haka! Duk duniya ba abin da ya kai sallar dare dadi, da azzalumai sun san dadin da muminai ke ji a Tahajjud, da sun ce ba su yarda a yi ba!" (Malam, Malam ne, 07).

Ko ban karkare ba, anan za mu gane tsabar Gwagwarmayar da Shaikh (H) ya sha da Tahajjud ne ya sa ta zamo masa tamkar Zuma mai zaki, ko Nono mai gardi.

AZUMIN NAFILFILI:

Gwagwarmayar Shaikh Zakzaky (H) a fagen Mujahadar azumin nafilfili bai misaltuwa. Domin:-

Yana Azumin dukkanin ranakun Litinin da Alhamis na tsawon shekara.

Yana Azumin kwanaki 50 a jere, tun daga daya ga watan Al-Muharram har zuwa ranar Arba'een na shahadar Imam Hussaini (As), wato 20 ga Safar. Watakil ranar Ashura ce kawai ba ya azumi a jerin wadannan kwanakin.

Yana Azumin watanni uku a jere, Rajab, Sha'aban, da Ramadan ba tare da ya sha ruwa ko na rana daya a cikinsu ba.

Yana Azumin kwanaki 9 na farkon watan Zulhajj na kowace shekara a jerensu.

Yana Azumin dukkanin ranaku masu albarka na shekara, ko mu ce ranakun munasaba, kamar ranar Mubahala, Ghadeer, Mab'ath, Dahwil-Ard, da dukkanin ranakun haihuwar Ma'asumai (SA).

A jimlace, nazari ya nuna cewa Shaikh Zakzaky (H) yana Azumi akalla 260 a cikin kwanaki 360 na shekara! Wace Gwagwarmaya da ruhi a fagen ibada ta fi wannan??

"Wani da suka yi zaman fursuna da Shaikh Zakzaky a kudu ya fadi cewa; "Lokacin da muka yi zaman kurkuku, Malam ya kwashe wata tara cur a jere yana Azumi!". (Malam Zakzaky: Rayuwarsa da Karamominsa, 10).

KARATUN KUR'ANI:

A duk karance-karancen duniya, ba karatun da Shedan ya tsana irin karatun Alkur'ani. Shi kuma Shaikh Zakzaky (H), ba karatun da ya fi so da kauna kamar karatun Alkur'ani!!

Marubucin littafin 'Tarihin Harkar Musulunci' yana cewa; Sayyid (H) ya kasance mai yawan karatun Alkur'ani, akwai ma lokacin da yake cewa; lokacin da yake zaune a kurkuku, yakan so ya sauke Alkur'ani a kasa da kwana uku, (wato yana so kullum ya sauke Alkur'ani cikin awa 24), amma tunda Sunnah shi ne karancin sauka kwana uku ne, to dole yakan hakura ya tsaya kan haka!" (Duba shafi na 26).

Ko da Shaikh Zakzaky ke rayuwa a gida cikin iyalansa, gami da dawainiyoyi da rashin lokaci, Malama Zeenat ta ce yakan sauke Alkur'ani ne cikin kwana 7, wato mako guda!!

A wannan Gwagwarmaya da ake yi tsakanin mai yin karatun Alkur'ani, da makiyin karatun Alkur'ani, wa ya yi Nasara??

GWAGWARMAYARSA DA AZZALUMAI:

Babin Gwagwarmayar Shaikh Zakzaky (H) da Zalunci da Azzalumai, shi ne babin da ya fi kowane babin gwagwarmayoyinsa fadi da tulin abubuwan fada da na nazari, watakil ma shi ne asalin maudu'in da aka ba ni ake so in yi magana akai.

To Amma, shi wannan babi din sanannen batu ne ga kowa, har ga na nesa da na kusa, yaro da babba, bature da balarabe, kirista da musulmi, Anne da kahiri, Kai duk wanda ya san sunan Zakzaky ma, to tare da wani bangare na Gwagwarmayarsa da azzalumai yake sanin sunan.

Dan haka, ba zan bata lokaci a nan ba, kawai darasin karatun kowa zai fitarwa kansa.

DARASI A GWAGWARMAYARSA DA AZZALUMAI:

Akwai dimbin malaman addinin Musulunci a kasar nan, amma shi kadai ke kira ga komar da rayuwa karkashin inuwar littafin Allah.

Akwai dimbin Shakashakan addini a kasar nan, amma shi kadai ne ba ya dasawa da gwamnati.

Akwai dimbin malaman addini a kasar nan, Amma shi kadai hukuma ke hankoron kashewa, shi kadai ta tsana, shi kadai take son kawarwa.

Shi kadai gwamnatin Nijeriya ta taba kamawa har sau goma tana tsarewa.

Shi kadai gwamnatin Nijeriya ke kashe almajiransa, da rusa gine-ginen Da'awarsa, da kashe 'ya'yansa, da kashe danginsa, da rushe wuraren karantarwarsa, da hana mabiyansa da yawa daga hakkoki na 'yan kasa.

Ba shi kadai ne malamin addinin Musulunci ba, amma shi kadai ke fadawa gwamnati gaskiya, shi kadai ke iya nuna adawa da duk wani shirin gwamnati na kokarin zaluntar 'yan kasa ko jefa su cikin mawuyacin hali!!

Tambaya a nan ita ce, me ya sa wadannan abubuwan ga Shaikh Zakzaky kawai suke faruwa???

In ka laluma, takaitacciyar amsar da za ka samu shi ne; DON SHI YANA GWAGWARMAYA DA ZALUNCI DA AZZALUMAI NE!!!

GWAGWARMAYARSA A WASU FANNONI:

Bangarorin Gwagwarmaya a rayuwar Shaikh Zakzaky (H) ba su da iyaka, sai dai mutum ya fadi iya wanda ya sani ko wanda zai iya tunawa.

Ba mu da isasshen lokaci na bin fannonin gwagwarmayar Shaikh Zakzaky daya bayan daya don yin tsokaci a kansu, duk kuwa da cewa su ma suna da muhimmancin gaske, kamar;-

GWAGWARMAYARSA DA AL'ADUN AL'UMMARSA:

GWAGWARMAYARSA A FAGEN KARE HAKKIN MATA:

GWAGWARMAYARSA WAJEN SHIRYAR DA AL'UMMA:

GWAGWARMAYARSA DA AZZALUMAN MAHUKUNTA:

GWAGWARMAYARSA A FAGEN SAITA ALMAJIRINSA:

Da ma dai sauran fannoni da dama.

Amma za mu iya wadatuwa da dan abin da muka ambata cikin wadannan mintuna wajan daukar darasi koyi. Madalla da hadisin da ya ce "Khairul Kalami, Maaqalla Wadalla".

DARUSSA DAGA GWAGWARMAYAR SHAIKH ZAKZAKY (H):

Akwai tarin darussa masu yawa abin koyi garemu daga gwagwarmayoyin Shaikh Zakzaky na rayuwa.

Bari mu dan yi mulahazozin wasu darussa a takaice don mu la'akartu da su.

HIMMA DA KWAZO:
Wani abin koyi daga rayuwar Jagora (H) shi ne himma da kwazo, tun tasowarsa bai san kasala, kiuya, da mutuwar zuciya ba, mutum ne mai kazar-kazar a fagen ayyuka, neman halal, neman ilimi da yawan ibada.

Kuma yakan hada Taura biyu zuwa uku ne a lokaci guda, ga neman ilimi, ga neman na dogaro da kai, ga kuma ibada.

DOGARO DA KAI:
Masana halayyar Dan Adam sun ce mutum ba ya zama cikakken mutum sai ya zama mai dogaro da kansa.

NEMAN ILIMI:
Awai babban darasi na koyi garemu daga Jagora (H) a fannin neman ilimi, da ma shi ilimi ba ma bukatar mutum ya tsaya fadin falala da muhimmancinsa.

Ko ba komai nemen ilimi ya fi Sallah, ya fi Azumi, ya fi Jihadi, kai ya ma fi Shahada!!

Imam Baqir (As) Yana cewa; Tawadar Malamai ta fifici jinin Shahidai" (Wasa'il, 2, 237).

Wannan ba wani abu ne da zai girmama a kwakwalwa ba, domin ai malami ne ke samar da Shahidi, ba dan an samu Malam a Zariya ba, da ba a samu Shahidi ko daya a Nijeriya ba!!

YAWAN IBADA:
A kowane runtsi da wuya,  Jagora (H) ba ya sakaci da ibada, mutum ne da ya wajabtawa kansa Nafila, ya farlantawa kansa Mustahabbi, yake tilasta kansa yin abubuwan da ba tilas ba.

RIKO DA ADDINI:
Riko da koyarwar addini da yin addini a komai namu, shi ne mafi girman darasin da rayuwar Jagora da Gwagwarmayarsa ke koya mana.

Dabi'un mu, ayyukanmu, zantukanmu, Action dinmu, Reaction dinmu, duk ya kamata su rika dacewa da addini bakin gwargwado.

FADA DA ZALUNCI:
Daga cikin abin koyi babba a gwagwarmayoyin Shaikh Zakzaky (H) akwai fada da Zalunci da danniya, dole mu koyi kin yin shiru, kin kauda kai, da kuma nuna yatsa ga duk wani yunkurin zalunci, ya'alla gare mu ne ko ga wasunmu, ya'alla Azzalumai ne za su yi zaluncin ko a cikin ya mu- ya mu ne!!

Malama Zeenatuddeen tana cewa; Zaluncin farko da ya kamata mu fara yaka mu kawar da shi, shi ne zaluncin cikinmu kafin na Azzalumai!!"

Kenan duk zalunci zalunci ne, ba sai in azzalumin mahukumci ne ya yi shi ba, hatta a group din WhatsApp ana zalunci, a hukunci tsakanin mutum biyu ana zalunci, a magana da baki ana zalunci, dan haka kowane dayanmu dole ya koyi nunawa zalunci yatsa, sam addini bai yarda da yin shiru da kauda kai ga zalunci ba, kuma wannan daya ne daga cikin manyan darussan da gwagwarmayar Shaikh Zakzaky (H) ta koya mana.

KAMMALAWA:

Kamar yadda na fadi tun farko, ba lallai ne ya zama na hau maudu'in a yadda aka tsammata ba, hasali ma na san da yawa ba za su zaci wadannan abubuwan da suka sanin ne za a maimaita a wannan maudu'in ba, a yi hakuri da hakan.

Allah ya yi dadin tsira da aminci ga Manzon Rahma da iyalan gidansa tsarkaka, da wadanda suka yi riko da tafarkinsu zuwa ranar Alkiyama.

Haazha Huwa Maa'indy, Wabillahit-Taufeeq!

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

MANAZARTA:

HARKAR MUSULUNCI
Na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

TARIHIN HARKAR MUSULUNCI.
Na M. Muhammad Sulaiman Kaduna

SHAIKH ZAKZAKY IKON ALLAH.
Na Cibiyar Wallafa da yada Ayyukan Shaikh Zakzaky.

🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏