Az~Zahra Badamasi Ishaq✍🏼
Kaduna Press

Hakika Musulunci ya haifar da gagarumin sauyi a tarihin mace, wadda har ya zuwa yau ba a samu na biyunsa ba. Domin ta hanyar sa ne, ta samu damar dawo da mutunci da hakkokinta da aka raba ta da su a karkashin zaluncin zamanin jahiliyya na karnoni da dama. Ta haka ne Musulunci ya kwato mata hakkokinta ta yadda za ta yi rayuwa cikin mutunci karkashin tsarin rayuwa mafificiya.

A karo na farko a tarihi, mace ta samu damar amfana da hakkokinta na dan'Adamtaka a karkashin tsari da dokoki irin na Musulunci. An yaye wa mata kangin zalunci, kana kuma ta samu damar rayuwa a matsayin dan'Adam mai mutunci, daukaka kana mai matsayi kamar dai-dai da na namiji. To amma fa dole ne wannan 'yanci ya kasance cikin iyakokin Allah Madaukakin Sarki Wanda Ya ba wa mace dama, kana kuma Ya tsara mata hanyar da za ta iya ba da nata gudummawar wajen gina rayuwa, daukaka, tabbatar da gaskiya da kuma yada alheri.

To hakika wannan kuduri zai kasance ne kawai kamar wani mafarki da tatsuniya a wajen wadansu, idan har ba a karfafa shi da wasu ayoyi na Alkur'ani mai girma da hadisan Annabi da kuma Mutanen gidansa (Ahlulbait) tsira da amincin Allah su tabbata a gare su ) ba.

(1) A zamanin jahiliyya, al'umma tana ganin mace a matsayin wata bi-tsami, wani abu na la'ana, matatta-rin muggan ayyukan shaidan, ko kuma sukan kwatanta ta da matsayin wata dabba da aka halicce ta a yanayin dan'adam. To amma ko da Alkur'ani ya zo sai ya karyata wannan kuduri, wanda ya saba wa gaskiya da kuma hakika. Ya ci gaba da nuna cewa namiji da mace wasu irin 'yan tagwaye ne da suka fito daga mabubbuga da kuma manufa guda.

" Ya ku mutane ! ku bi Ubangijinku da takawa, Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata." ( Surar Nisa'i: 4:1)

" Shi ne Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya sanya daga gare ta, ma'aurata, domin ya natsu zuwa gare ta." (Surar A'araf: 7:189)

"Kuma Allah Ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma Ya sanya muku daga matan aurenku diya da jikoki...."(Surar Nahali: 16:72)

Bayan bayyana matsayin mace a rayuwa da kuma samuwar dan'adam a fili, Alkur'ani mai girma ya yi kakkausar suka ga al'adar nan ta bisne 'ya'ya mata da rai, wato Wa'id[1]

"Kuma idan wadda aka turbude ta da rai aka tambaye ta, saboda wani laifi ne aka kashe ta?"(Surar Takawir:   81:8-9)

Kana kuma ya kawo karshen zamanin da ake kange mace daga aure har sai ta biya kudin fansar kanta ko kuma cikin zalunci a gaje ta bayan mutuwarta.

" Ya ku wadanda suka yi imani ! ba ya halalta a gare ku, ku gaji mata a kan tilas. Kuma kada ku hana su aure domin ku tafi da sashen abin da kuka ba su."(Surar Nisa'i: 4:19)

Sannan kuma ya yaye musu irin zalunci da wulakanta su da mazaje suke yi. Don haka ne ma Alkur'ani ya ba da muhimmanci mai girman gaske kan tausaya musu yayin mu'amala da su:

"Kuma ku yi zamantakewa da su da alheri. Sa'an nan idan kun ki su, to, akwai tsammanin ku ki wani abu, alhali kuwa Allah Ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa."(Surar Nisa'i: 4:19)

Koda yake a da, talauci ma ya kan sa mutane su kashe 'ya'yayensu musamma ma 'ya'yaye mata, don haka Alkur'ani ya kawar da wannan al'amari ( daga kanta):

" Kuma kada ku kashe diyanku saboda talauci, Mu ne Mu ke arzurta ku da su."(Surar An'ami: 6:151)

Kana kuma Musulunci ya bayyana cewa ma'aunin daukaka ba wai ya dogara kan mazantaka ba ne face kan imani (da Allah) da ayyuka na kwarai. Duk wanda ya aikata wani aiki to zai sami sakamakonsa, shi namiji ne ko mace:

" Lallai Musulmi maza da Musulmi mata da Muminai maza da Muminai mata, da masu tawali'u maza da masu tawali'u mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu hakuri maza da masu hakuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata, da masu tsare farjojinsu maza da masu tsare farjojinsu mata, da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonSa da yawa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma." (Surar Ahazabi: 33:35)

Kana Musulunci ya ci gaba da nuna cewa muminai sashensu majibincin sashe ne. Sun kasance masu yada alheri a tsakaninsu kana suna umurni da abu mai kyau, sannan suna hani da munana:

" Kuma Muminai maza da Muminai mata, sashensu majibincin sashe ne, suna umurni da alheri kuma suna hani daga abin da ba a so, kuma suna tsayar da salla kuma suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa. Wadannan Allah Zai yi musu rahama." (Surar Tauba: 9:71)

Hakika Musulunci ya tsaya wajen bayyana irin yanayin mu'amalar da ke tsakanin mace da namiji ta hanyar aure :

" Su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su" (Surar Bakara: 2: 187)

" Kuma akwai daga ayoyinSa, Ya halitta mu ku matan aure daga kanku, domin ku nitsu zuwa gare su, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku." (Surar Rumi : 30:21)

Baya ga tsara dokoki kan hakkokin da 'yancin mace, hakika Alkur'ani mai girma ya mai da hankali kan wajibcin girmamawa da kuma kulawa gare ta, kana da kuma bata cikakkun hakkoki da 'yancinta.

Manzon Allah, Muhammad (s.a.w.a ) yana cewa :

"Babu wadanda za su girmama mata, face masu mutunci, kana babu wadanda za su cutar da su face marasa mutunc[2])"

"Kada ku nuna bambanci wajen kyauta a tsakanin 'ya'yayenku, hakika da za a ba ni zabi wajen taimako, lalle da na zabi mata ( don taimaka musu)[3]"

"Ba na tsammanin mutum zai samu karuwa a imaninsa, ba tare da kaunar mata sosai ba[4]"

Sannan bugu da kari, akwai tsarkakan nassosi masu yawan gaske da suke kira da a tabbatar da mace a kan matsayin da take da shi a cikin al'umma.

Kana kuma Musulunci ya ba da wasu muhimman abubuwa ga mace. Ya tsara mata sutura ta musamman don tabbatar da daukakarta da kuma kare mata mutuncinta daga lalacewa da rugujewa. Don haka ana iya cewa ta hanyar hijabi (Lullubin Musulunci), Musulunci ya sami cim ma manyan manufofi guda biyu:

Na farko, ya kare mata akidarta, yayin da take aikata abubuwan da suka hau kanta na wajen ba da gudummawarta ga al'umma, ci gaba da kuma Sakon Musulunci da kuma gudanar da al'amurran da suka shafi rayuwarta gwargwadon yadda Musulunci ya tsara.

Na biyu, yana kare tsarkakan mace da kuma toshe duk wata hanya da za ta kai ga aikata duk wani aiki da zai kai ta ga fadawa ga munanan ayyuka; ko kuma ya juya ta ta zama wani makami da ke lalata al'ummar da take rayuwa a cikinta -kamar yadda yake faruwa a kasashen Turai -. Baya ga irin nasarar da hijabi ya samu wajen kare mace da kuma tsara mata irin suturar da za ta sa da kuma haramcin da Musulunci ya yi na cakuduwan (mata) da wadanda ba muharramansu ba, da dai sauran ka'idoji, za mu ga irin matukar kokarin da Musulunci ya yi wajen kare namiji da mace, da kuma dukkan al'umma, daga yaduwar munanan ayyuka da kuma rayuwar da ba ta da amfani.

Dangane da wadannan ka'idoji da dokoki, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:

Dangane da wadannan ka'idoji da dokoki, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Ka ce wa Muminai maza da su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. Kuma ka ce da Muminai mata da su kawar da idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi, kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazajensu ko ubanninsu, ko ubannin mazajensu, ko diyansu, ko diyan mazansu ko 'yan'uwansu, ko diyan 'yan-'uwansu mata ko matansu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai wadanda ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi duka da kafafunsu, domin a san abin da suke boyewa daga kawarsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya, Ya ku Muminai!, tsammaninku ku sami babbar rabo". (Surar Nuri: 24:30-31)

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, kana tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu (s.a.w.a) da Mutanen gidansa tsarkakku (a.s.).