An haifi Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky a cikin birnin Zariya, a ranar 15 ga Sha’aban 1372 (May, 1953).

Iyayensa Malaman Alkur’ani ne, suna karantarwa da kuma yin noma a matsayin hanyar gudanar da rayuwa. Don haka Shaikh Zakzaky yana tasowa ya fara karatun Alkur’ani a wajen Mahaifinsa.

A daidai lokacin da yake karatun Alkur’ani a wajen mahaifinsa, an kuma saka shi a wata makarantar Alkur’ani a lokaci guda, yana zuwa makaranta yana kuma yin karatu a gida. Sannan kuma yana raka mahaifinsa tare da ‘yan uwansa zuwa gona don aiki.

A ka’idar gidan su Sayyid Zakzaky a wancan lokacin sai yaro ya sauke Alkur’ani sannan yake saka littafan addini ya karanta a zaurukan Malamai. Don haka lokacin Shaikh Ibraheem Zakzaky yana dan shekaru 14 ya sauke Alkur’ani, nan take ya saka littafai ya fara karatun addini a wajen Mahaifinsa, mahaifiyarsa da kuma wasu Malamai a zaurukansu a cikin birnin Zazzau.

Shaikh Zakzaky ya karanta fannoni daban-daban na Luga, Nahawu da Sarfu, Fiqihu da Tafsirin Alkur’ani da sauransu. Tun bai fi shekaru 20 da haihuwa ba ya karance littafan da ake karanta su a zaurukan ilimi a kasar Hausa, irinsu Ajuruma, Murha, Saja’I, Alfiyan Danmaliki, da wasu littafan da suka shafi Luggan Larabci kamar Ishiriniya, Witiriya, Ashariya har ma da Makamatul Hariri da Shu’ara’ul Jahiliyya. Haka ma a bangaren Fiqihun Malikiyya, Shaikh ya kai ga sauke har Muktasar a wannan lokacin.

A shekarar 1969 (lokacin yana dan shekaru 16), wato bayan ya sauke Alkur’ani, a lokaci guda yana yin karatun littafai a zauruka, sai kuma aka saka shi a makarantar Nizamiyya, Inda ya fara da wata makaranta ta koyon Larabci a nan Zariya, wacce ake kiranta Zaria Provincial School. Bayan shekaru biyu, wato 1969 zuwa 1971 ya kammala ta.

Bayan kammala wannan makarantar a Zariya, sai Shaikh Zakzaky ya tafi wata makaranta da ake ce mata Madarasatul Ulumul Arabiyya (School for Arabic Studies) a Kano, inda ya fara ta daga shekarar 1971 ya kammala a shekarar1975.

A wannan makaranta ta SAS, Kano, ana tarbiyar Malamai ne don su je su koyar a mataki mafi inganci a makarantu a bangaren Larabci da addini. Don haka an fi karfafa karatun addini a cikinsa. Amma sai ya kasance akwai wasu ‘Advance Level’ da mutum yake da zabi ya jona su da karatunsa, sai ya rika zuwa anai musu ‘lesson’ dinsu da yamma (wato ba a ainihin lokacin makarantar ba). Kuma mutum na iya zana jarabawar shiga Jami’a daga wannan karatun ‘Advance level’ din.

Malam Zakzaky a wannan lokacin, bisa zabin kansa ya jona wannan ‘Advance level’ din, inda ya karanta darussan da suka hada da English literature, Economics, Government, Hausa, Arabiyya da kuma Islamic studies.

Bayan kammala makarantar, sai ya zana jarabawar ‘Grade II Certificate’, sannan kuma ya zana jarabawar wadannan darussan da ya yi a ‘Advance Level’ din. Sai ya zama ya zana jarabawa kashi biyu, kuma duk biyun suka fito a kusan lokaci guda duk ya ci su. Wato ya ci jarabawarsa ta Grade 2, ya kuma ci Jarabawar da ya yi na wasu fannoni guda hudu, wato Economics, Hausa, Government da kuma Islamic Studies.

Fitowar wannan jarabawar ta Advance level a shekarar 1976 kuma ya zama ya ci, wannan ya bashi damar fara karatun Jami’a kai tsaye ba tare da share fage ba. Inda ya fara karanta Economic, Government da Sociology. Daga baya sai ya fi kwarewa a Economics, don haka sai ya dauke shi a matsayin ‘course’ dinsa. Ya yi ‘Degree’ a bangarensa, inda ya kammala a shekarar 1979.

Karatun Shaikh Zakzaky na Nizamiyyah, daga farko har kammala ‘Degree’ dinsa na farko ya yi su ne a shekaru 9 kacal.

— Fara Harkar Musulunci A Jami’a

A karshen 1970s, bayan da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya shiga Jami’ar a 1976, da yake dama shi ma’abocin addini ne, don haka ya tsintar da kansa a cikin kungiyar dalibai Musulmi wacce ake kira MSS a lokacin, kuma ya kasance har ma an wayi gari Shaikh Zakzaky (H) shine babban sakataren kungiyar ta MSS reshen ABU. Sai kuma ya zo ya zama mataimakin shugaban kungiyar ta MSS na kasa baki daya mai kula da harkokin kasashen waje.

Sai ya zama a daidai lokacin da akwai musayar ra’ayoyi dangane da abin da ya kamata ya zama makomar kasa. Wato me wane tsari ne ya kamata ya zama shi ke tafiyar da kasa da mutanenta? Ana ta tafka muhawara a tsakanin dalibai, har ya zama kamar daliban jami’a da Malamansu a lokacin sun kasu kashi uku:

1- Masu Ra’ayin Kwaminisanci: Da yawan dalibai masu ganin sun waye, da lakcarori, kwaminisanci suke yi. Suna sukan addini gaba daya, da kuma sukan addinin Musulunci musamman kan cewa addini kawai an samar da shi ne ma don a samu damar mulkan mutane.

Kwaminisawa sun rika sukar addinin Musulunci ta hanyar ba da misali da mulkin wasu sarakuna da daulolin Gargajiya ko na Musulunci, irin su Mulkin Banu Umayya da Banul Abbas da irin ta’addancin da Sarakunansu suka yi a tarihi. Haka ma da irin mulkin sarakunan Gargajiya a kasar Hausa. Sai suke nuna cewa wannan zaluncin da sarakuna suka rika yi shine koyarwar addinin Musulunci. Don haka suna ganin ba zai taba yiwuwa addini ya zama tsarin adalci ga rayuwar mutane ba. Har ma suna cewa addinin Musulunci ya kafu ya yi iko ne a duniya saboda lokacin duniya bata waye ba.

2- Kungiyar dalibai Kiristoci (FCS): Sune gungu na biyu a Jami’a a wancan lokacin. Suma suna da nasu ‘view’ din, na cewa sun amince ne kan ya zama an cigaba da tafiya a kan nizamin da ke iko da kasar nan. Ko ba komai shi nizamin da ke iko da kasar yace ba ruwansa da addini. To kuma suma a wajensu addini daban ne rayuwar mutum daban. Shi addini tsakanin mutum ne da Ubangijinsa, rayuwa kuma daban. Don haka suna marawa tsarin da ke tafiya baya.

A lokaci guda suna sukan addinin Musulunci shigen irin sukan Kwaminisawa, cewa ayyukan Sarakuna da dauloli shine addinin Musulunci.

3- Kungiyar Dalibai Musulmi (MSS): To, sai ga Shaikh Zakzaky da nashi matsayar ta daban, cewa matsayar kungiyar Musulmi shine tabbas duk zargin da bangarori biyun suke jinginawa addinin Musulunci korarre ne. Inda ya rika shirya lakcoci daban daban na fadakarwa, da yin martani ga Kwaminisawa da Kiristoci akan cewa addini saukakke ne daga sama, kuma masu aiki da shi suna bambanta, ba komai bane idan Musulmi ya yi sunanshi Musulunci, saboda haka abubuwan da su Sarakuna da Daulolin suka yi da yawa ya sabawa koyarwar addini, don haka ba shine Musulunci ba.

Shaikh Zakzaky ya rika wanke addinin Musulunci da cewa a kawo inda aka ga zalunci a tarihin gwamnatin da Manzon Allah (S) ya kafa! Ya kuma rika tabbatar wa da mutanen jami’a cewa komawa ga addinin Musulunci shine kadai mafita wajen samun adalci da wadatuwar arziki da samun aminci. Daga irin haka ne ya fara kira ga komawa ga addinin Musulunci, da yunkurin tabbatar da shi ya yi iko a doron kasa.
Shaikh Zakzaky ya tsaya kyam a jami’a wajen fadakar da dalibai da Malamai cewa Musulunci kammalallen nizamin rayuwa ne ga mutum, addini ne, hanyar rayuwa ne, kuma ‘ideology’ ne a lokaci guda. Kuma a kan asasin adalci da ilimi da hujja aka kafa Musulunci. A yayin da shi Kirista yake ganin cewa Addini daban rayuwa daban, Musulunci na ganin duk abu guda ne. Kwaminisanci na ganin ana danniya suna bukatar a kawo adalci. To Shaikh Zakzaky ya tabbatar musu da cewa ba inda za a samu adalci in ba a Musulunci ba.

Shaik Zakzaky ya rika wannan ne ta hanyar shirya Lakcoci, da fadakarwa a yayin tarukan IVC na dalibai Musulmi da rubuta ‘articles’ a raba ko a manna su, da sauransu.

Wannan ya maido da hankalin hukumar jami’ar kan Shaikh Zakzaky da wadanda suke tare da shi a wannan ra’ayin. Ko ba komai, da hukumar tana ganin ‘Yan Kwaminis a matsayin barazana, don haka akan takura musu a hana su gama karatun ko wucewa gaba, ai ta rike su, saboda ana ganin fitansu daga Jami’a barazana ne ga nizamin da ke iko da kasar, tunda suna da burin ya zama an canza shi da wani ne.

To, amma da suka ji ga kuma abin da wasu Musulmi suke cewa, suna raddi ga Kwaminisawa da ‘yan FCS, suna kuma cewa ma a dawo ma addinin Musulunci, shine tsarin adalci. Sai hukumar ta dauka cewa to yanzu wadannan Musulmin sun fi ‘yan Kwaminis zama hadari ga kasa. Don haka ta fara daukar matakai a kansu, na mutum yaci jarabawa ace atafau bai ci ba, ko kuma ma a kore shi. Sai aka zo ma ta fara sa a kama mutum a daure a kurkuku.

A daidai lokacin da Shaikh Zakzaky ke zana jarabawar kammala Jami’ar, ya zana jarabawa guda 1 saura guda hudu, aka kama su, saboda wannan ‘struggle’ din da suke yi na addini. Ya zama an gama jarabawar suna tsare. Sai daga baya aka sako su, aka dawo aka musu jarabawowin, ta yiwu hukumar na tunanin ba za su ci ba, amma sai suka ga yaci jarabawar baki-daya, don haka sai suka rike masa sakamakon. Yau din nan shekaru 40 jami’ar Amadu Bello bata bashi takardar shaidar kammala digirinsa ba.

— Bayan Kammala Jami’a:

Bayan kammala Jami’a, Shaikh Zakzaky ya cigaba da gabatar da gwagwarmayarsa na yunkurin tabbatar da addinin Musulunci. Tun a shekarar ta 1979 ta bayyana balo-balo cewa akwai wata da’awa da ke kira a komawa tsarin addinin Musulunci. Sai dai tana jami’a ce kawai a tsakanin daliban jami’a, amma a waje ba a san da ita ba.

Ana wannan halin ne, kawai sai ga juyin-juya halin Musulunci na Iran a watan February 1979. Ga wani Malamin addinin Musulunci ya kira mutane zuwa ga komawa nizamin Musulunci, kuma ya fafata tsawon shekaru, har yau gashi ya juya kasar ya kori nizamin kafirci ya tabbatar da na Musulunci. Wannan ya karawa Shaikh Zakzaky da masu ra’ayinsa kwarin guiwa sosai, cewa lallai wannan abin da suke da’awarsa mai yiwuwa ne in har sun dake.

Juyin Musulunci na Iran ya kuma ba da amsa ga masu ganin cewa ba zai yiwu addinin Musulunci ya dawo yai iko da mutane ba, a yayin da ga wani Malami ne, amma ya jagoranci yunkuri har ma ya tabbatar da Musuluncin. ‘Revolution’ din Iran kamar yadda Shaikh Zakzaky ya sha fada, ya kara masa kwarin guiwa sosai a wannan lokacin, cewa abin da suke kira a kai din nan fa mai yiwuwa ne.

— Bayan Juyin Musulunci A Iran

Bayan Juyin Musulunci a Iran, a shekarar 1980 Shaikh Zakzaky ya samu ziyartar Jamhuriyar ta Musulunci ta Iran, inda har yai dacen samun damar ganawa da Imam Khumaini (QS) a lokacin yana gadon asibiti. Imam ya yi musu jawabi, har ma Shaikh Zakzaky ya yi ‘recording’ din jawabin ya yo guzurinsa. Wannan ma ya kara wa Shaikh Zakzaky kwarin guiwa sosai da karin shaukin jin cewa lallai dawowar ikon addini ba abu ne mare yiwuwa ba.

Don haka bayan dawowar Shaikh Zakzaky daga Iran, aka rika shirya lakcoci a jami’o’i yana zuwa yana jawabi a kan abin da ya gani da abubuwan da suka burge shi a jamhuriyar Musulunci ta Iran. Shaikh Zakzaky ya fara da jawabi a jami’ar Lagos, ya je Ibadan, sannan Ilori, sai Jos, sai Maiduguri, yayi a Jami’ar Bayero ta Kano, da jami’ar Sokoto, da sauran jami’o’in Nijeriya. Haka ma a ABU da ya gabatar, mutane sun cika sosai, sun rika zuwa daga wurare mai nisa don sauraron wannan tsarabar.

— Shelar Da’awa A Garin Funtuwa:

Da yake bayan fara dagowar Harkar ta Musulunci, ko da yake Shaikh Zakzaky ya kammala karatun jami’a a sannan, sai dai kuma magoya bayan Harkar daga cikin dalibai ba su tarwatse ba, sun cigaba da yin wasu tarurruka don karfafa juna a kan Musulunci, kamar tarukan IVC da tarukan karawa juna sani daban-daban. A irin wannan tarukan ne, a ranar 5 ga Mayun 1980 Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi shelar wannan da’awar a gaban dimbin jama’a a garin Funtua da ke jihar Katsina.

A nan ne Shaikh Zakzaky ya bayyana tawayensa ga tsarin kafircin da ke iko da kasar nan, ya kuma jaddada wulayarsa ga Allah (T) da ManzonSa da Alkur’ani. Inda ya shelanta aniyarsa na kira zuwa ga dawowa shari’ar Alkur’ani a kasar nan. An yiwa jawabin da ya gabatar a ranar take da ‘Funtua Declaration’.

Wannan ya bude sabon babi wa duniyar Harka Islamiyyah. Da tana cikin jami’a ce a tsakanin dalibai. Yanzu an shelantata ga kowa da kowa ma, an bayyana cewa yanzu da’awa ce da take bukatar kowa da kowa. Kun san kuwa hukuma ba za ta yi sake da irin wannan da’awa da yake mata barazana ba, don haka tun a wannan lokacin suka fara yunkurin kawar da Harkar da Shaikh Zakzaky daga doron kasa.

— Muzaharar Farko A Harkar Musulunci

Muzaharar farko da Harkar Musulunci ta fara shine wanda aka gudanar da shi a watan Afrilun 1980. Bayan juyin Musulunci a Iran, Amurka ta yi wani gagarumin shiri da nufin za ta kwato wasu jami’an ofishin jakadancinta da ke Iran, wadanda aka kama su a lokacin juyi. Amurka ta shirya sosai don kaiwa Iran hari ne da nufin murkushe ta. Sai Allah ya ba Iran ikon dakile duk wani shirin na Amurka, inda duk shirinsu ya rushe a wanan lokacin bisa taimakon Allah.

To, sai su Shaikh Zakzaky suka gudanar da Muzahara a garin Zariya inda suke bayyana murna da farin-cikinsu a kan rugujewar shirin Amurka na kaiwa Jamhuriyyar Musulunci ta Iran hari a daidai wannan lokacin. Sai ya zama wannan Muzaharar ta murnar kunyatar Amurka ta kasance Muzaharar farko a tarihin Harkar Musulunci.

Bayan ta ne kuma a farkon watan Mayu, 1980 aka yi Funtua Declearation, inda Shaikh Zakzaky ya shelanta wannan da’awar. Bayan nan kuma sai aka gabatar da muzaharar da akawa take da ‘ISLAM ONLY’, wacce ita ce Muzahara ta biyu a Harka Islamiyyan, amma ita ta fi shahara.

Muzaharar ISLAM ONLY, an yi ta ne a watan May, 1980 a Zariya, inda ‘yan tsirarun ‘yan uwa suka gudanar da ita, dauke da kwalaye da takardu masu rubuce da hadafin fitowa wannan Muzaharar, wato bayyana bukatar addinin Musulunci ya zama shi ke iko da kasar nan. Kuma ma har aka rika rubuta ISLAM ONLY a wasu bangwaye a lokacin, wanda sukai shakaru basu gushe ba.

Wannan Muzaharar ta shelantawa mutanen gari cewa yanzu ga wasu da suke cewa a koma ma addini. Sai dai kowa yana ganin ba abu ne da zai taba yiwuwa ba a yanzu. Don haka an rika yiwa su Shaikh Zakzaky kallon cewa kawai zafin kan daliban jami’o’i da yarinta ne ke dibansu.

Muzahara ta zama daya daga cikin abubuwan da Harkar Musulunci ke gabatarwa wajen isar da sakonninta. Izuwa yanzu Harkar na gudanar da Muzaharori zaunannu kamar Muzaharar Quds, Ashura, Maulud, da kuma masu bijirowa kamar Muzaharar Allah wadai kota nuna goyon bayan wani abu da ya faru a duniyar Musulunci.

— Fahimtar Mazhabar Ahlulbait (AS):

Ko da yake babu takamaiman masaniya a kan hakikanin lokacin da Shaikh Zakzaky ya fara bin Mazhabar Ahlulbait (AS), sai dai kuma bayyanar Shi’anci a cikin Harkar Musulunci ya yi karfi ne a gab da tsakiyar shekarar 1995, inda har ma wasu daga almajiran Shaikh Zakzaky suka balle daga bin da’awar tasa a shekarar 1994 bisa hujjar cewa su ba za su yi Shi’anci ba.

Sai dai kuma a tsawon shekarun da’awar Shaikh Zakzaky, ba yana kira zuwa ga wata Mazhaba ko fahimta bace, face kira ne zuwa ga Musulunci da kokarin tabbatar da shi a doron kasa, yunkurin kawar da zalunci da azzaluman da suka mai da dukiyar kasa kayansu, suke sarayar da shi ga kasashen yammcin duniya bisa zalunci.

Ko da yake mafi yawan almajiran Shaikh Zakzaky suna bin Mazhabar Ahlulbait (AS), amma hakan bai kange mabiya Mazhabar Ahlussunah da ma mabiya wasu Darikun kasancewa magoya bayansa ba. Cikin magoya bayan Shaikh Ibraheem Zakzaky da da’awarsa a yanzu har da Kiristoci da Malamansu, wanda aka hadu da su a fagen yunkurin neman yanci da kawar da zalunci.

— Yunkurin Kawar Da Harkar Musulunci

Shekara guda da Muzaharar ISLAM ONLY, a watan Mayun 1981 Shaikh Zakzaky ya halarci wani taro a Sokoto, inda ya yi jawabi a kan addinin Musulunci da bukatuwar dawowarsa ya yi iko da doron kasa. Bayan kammala taron jami’an tsaro suka kama Shaikh Zakzaky da wasu ba’adin ‘yan uwa, aka kai su gaban Kurkuku, ba tare da shari’a ba bare a basu damar daukar lauya, kawai aka ce an yanke musu hukuncin dauri na shekaru uku. Wannan ne kamun Shugaban kasa Shagari, wanda aka daure Shaikh Zakzaky tsawon shekaru uku. Daga May 1981 zuwa May 1984 sannan aka sake su.

Shaikh Zakzaky yana kurkukun nan Buhari ya yi juyin mulki ya hambare Shagari. Don haka sai ya fito a lokacin Buhari na mulkin Soja. Sai dai kuma watanni shida bayan fitowarsa daga Kurkukun, sai kuma Buhari a lokacin yana yayin kame-kamen manyan mutane ya daure, nan ya sake kama Shaikh Zakzaky ya daure shi.

Buhari ya kama Shaikh Zakzaky ne a watan Disambar 1984, lokacin Shaikh din bai jima da aure ba, don haka ma har aka haifawa Shaikh Zakzaky yaronsa na farko da aka saka ma suna Muhammad, Shaikh din na tsare a kurkukun Janaral Buhari. Buhari bai bayyana dalilin kamu da tsarewar ba, face kawai saboda wai matsalar tsaro. Kamar dai yanzu da ya kuma kama Malam din, ya tsare shi wai da sunan matsalar tsaro.An saki Shaikh Zakzaky ne a watan Agustan 1985, bayan an hambare Buhari daga mulki. Wato bayan ya shafe watanni kusan 9 a wannan kurkukun.

Shaikh Zakzaky ya samu hutun shekaru 2 a waje, inda ya cigaba da gwagwarmaya, har zuwa sadda Janar Babangida shima ya kama Shaikh Zakzaky ya daure na tsawon shekaru biyu. Bayan da ya fake da wani rikici da aka yi a Kafancan, sai ya tura aka kama Shaikh Zakzaky, aka kai shi wata kotu a Abuja, ta yanke masa hukuncin dauri. Don haka Shaikh Zakzaky ya zauna a Kurkuku daban-daban tsawon shekaru biyu a wannan kamun wanda ya kasance daga watan Maris din 1987 zuwa 1989.

Duk wadannan kame-kamen mahukuntan sun rika yinsu ne da nufin kawo karshen Harkar Musulunci da neman damar ganin bayan Shaikh Zakzaky. Sai dai kuma a duk sanda ya fito yana cigaba da gwagwarmayar ne, a yayin da kuma in yana tsare ‘yan uwa suna cigaba da yin komai kamar yana nan ba tare da fashi ba. Har ma ya kasance duk sanda ya fito daga kurkuku al’umma kan ninku a yawa ne wajen goyon bayansa.

A shekarar 1991 ma, Babangida ya kuma kama Shaikh Zakzaky, kamun da ya auku a filin jirgin saman Aminu Kanoa yayin da Shaikh din ke nufin zuwa wani taro a London. Sai dai duka-duka Shaikh Zakzaky bai fi kwanaki biyar a hannun hukumomi ba suka sake shi.

Daga shekarar 1991 ba a sake kama Shaikh Zakzaky ba sai a 1996 inda Janaral Sani Abacha ya kama shi, ya daure shi shekaru 2 da wata 3. Wato 1996 zuwa 1999, bisa zargin cewa, Shaik Zakzaky yace: “Babu Hukuma sai ta Allah.” Bayan mutuwar Sani Abacha, Shaikh Zakzaky ya fito a lokacin rikon kwaryar Abdussalam Abubakar.

Tun fitowar Shaikh Zakzaky a lokacin Abacha, harka ta rika habbaka, inda ta samu miliyoyin magoya baya. Ko da yake gwamnatoci daban-daban, musamman gwamnatin Umaru Musa Yar Adua da ta Goodluck Jonathan sun ta yunkurin dirarwa Harkar Musulunci da kokarin ganin bayan Shaikh Zakzaky, amma Allah na wargaza duk mugun kullinsu.

A watan July, 2014 sojojin Nijeriya sun budewa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky wuta a yayin da suke gudanar da Muzaharar goyon bayan Palasdinawa a garin Zariya, inda suka kashe mutane 34, ciki har da ‘ya’yan Shaikh Ibraheem Zakzaky guda uku, Sayyid Ahmad, Sayyid Hamid, da Sayyid Mahmud.

Sai a karshen shekarar 2015 Gwamnatin Buhari a mulkin farin hula, ta sake afkawa Shaikh Zakzaky, bayan ta kashe almajiransa da ‘ya’yansa da ‘yan uwansa kimanin mutum 1000, sannan suka harbe shi suka kama shi suka tsare shi, kusan shekaru hudu ana masa haramtacciyar tsarewa. A yayin da jami’an tsaron Nijeriya suka kashe fiye da mutum 100 daga magoya bayan Shaikh Zakzaky a yayin da suke fitowa Muzaharar kira a sake shi.

Shaikh Zakzaky ya zauna a Kurkuku daban-daban, lokacin Obasanjo Soja an tsare Shaikh ne a cell din Zariya na tsawon makonni. Shehu Shagari ya tsare Shaikh a Inugu, Buhari Soja ya daure Shaikh Zakzaky ne a Kurkukun Kirikiri a Lagos, Babangida kuma ya tsare Shaikh a Fatakwal, Abacha a Fatakwal da Kaduna, yanzu kuma Buhari a Abuja da Kaduna.

— Karkarewa:

A halin yanzu, kiran da Shaikh Ibraheem Zakzaky yake yi ya doshi shekaru 40 cur, a yayin da yake da magoya baya fiye da miliyan 20 a fadin Nijeriya da kasashen makwafta. Har ila yau, kusan kowane lungu a wannan duniyar an san Shaikh Zakzaky da da’awarsa, musamman ma bayan aukuwar kisan-kiyashin Zariya na Disambar 2015.

Shaikh Zakzaky na da mata daya, Malama Zeenah Ibrahim. Sun haifi ‘ya’ya tara, Muhammad, Nusaiba, Ahmad, Hamid, Suhaila, Mahmud, Hammad, Ali Haidaar da Humaid. Sai dai shida daga cikinsu sun yi Shahada, a yayin matan guda biyu da kuma Sayyid Muhammad ke raye, kuma harma yana da yaro guda mai suna Nadirul Husain.

Ana kiransa da ‘Sayyid’ saboda kasancewarsa Sharifi, jikan Manzon Allah Muhammad (S) ta tsatson Imam Hasan AlMujtaba (AS).

Allah Ya daukaka Harkar Musulunci da Shaikh Zakzaky.