Nasir Isa Ali.
--------------
KAFIN_YA_YANKE_HUKUNCI.
-----------------------------
Wata majiya dake kusa da shi H.J.Kolawole ta shaida min cewar,lallai ya shiga wani yanayi wanda bai taba shiga ba a tsawon shekarun da ya kwashe yana yin aikin alkalanci.Amma da yake mutun ne jajirtacce kuma nitsattse,sai ya iya fuskantar wannan yanayin har ya cimma gaccin da yake son ya cimma.
Bai samu tursasawa dayawa daga gwamnati kai tsaye ba,saboda daman tana rigama da wasu alkalai wanda take zargesu da cin hanci tare da kin yin gaskiya yayin yanke hukunci a wasu sharia.Kuma kungiyan lauyoyi da alkalai sun nuna tirjiya da rashin amincewarsu kan fadar da gwamnatin ke yi da wadancan alkalan.Ana kallon cewar kamar ita gwamnatin ce da kanta ke zagayawa tayi amfani da alkalan wajen danne wasu sai kuma ta zagayo tana kamasu tana tuhumarsu da yin mago mago a aikinsu.
Babban abu na farko wanda mai girma H.J.Kolawole ya fara fuskanta shine na, kiraye kiraye daga wasu manyan mutane na cikin kasar nan da kuma kasashen waje cewar,lallai yayi adalci kan wannan shari'a da aka kawo masa a kotunsa.Sannan kuma ya fahimci irin wannan shari'ar sosai.
Kuma lauyan da El-Zakzaky da matarsa suka dauka dan kwakwazo ne kuma yankin da suka fito daya ne,don haka in yayi murdiya ya san bashi ba zaman lafiya har abada. Yace wadanda ba musulmi ba sun fi kiransa da ziyartarsa domin nuna damuwarsu ga wannan sharia'ta El-zakzaky da matarsa.Kuma wasu alkalai da dama daga kasashen waje duk sun kirawo shi domin nuna masa irin muhimmancin shariar dake gabansa tare da nuna msa irin romon dake ciki idan yayi adalci.
Yace akwai ma wanda ya kirawo shi yana fada masa cewar shin ka san cewar ido da kunnen duniya na kan wannan shariar? Kuma ka san cewar kusan duk fadin duniyar nan an yi zanga zangar goyon bayan wannan mutumin ?(El Zkzaky)
---
Mai bamu labarin yace H.J.Kolawole ya samu sakonni ta email da sauransu daga wasu alkalan da kwararrun lauyoyi na taimakon wasu litattafai da sauran misalsalu na wasu shar'un da aka yi shigen na Mallam Zakzaky din nan.yace ya lura shi kansa (Kolawole)ya canza sosai wajen kara lokacin yin nazari da uma bitar shari'ar mallam Zakzaky idan ya dage ranar ya dawo gida. Yace ya sha mamaki yadda masu ilimi,mukami da yan kasuwa na yankin da ya fito suka rinka zabarinsa suna ja masa kunne da cewar kar fa yabi son zuciya kan wannan shariar har ya kai ga ya jefa yankin nasu cikin badakala ko wani abin kunya.Yan arewa ne ke yin mulki kuma sune suka kitsa wannan kisan kiyashin na Zaria to shi kuma ya yanke hukunci mai cike da adalci domin ya nunawa duniya cewar akwai masu hankaliba Najeriya.
----
Yace babban abinda ya fuskanta shine ziyarar da wasu jami'an gwamnatin Buhari ke yawan yi masa tare da gayyatarsa wajen taruka da cin abinci,zu kan zo gidana ko ofis da sunan wai sun zo gaisuwa da sada zumunci to ahakan ne suke samun damar shigar da bukatunsu a kaikaice na neman ayi murdiya a shariar.
Yace ya fuskanci wasu canje canje a ofishinsa na ma'aikatan wurin ta yadda suka lura da cewa hatta wani lokacin zuwa wani lokacin sai aga an jirkita masa wasu takardun ko fayil fayil din kotun.Wanda ke nuna cewar akwai masu bibiyar shariar idan kotun ta tashi.Don haka sai ya rinka kafa kafa da muhiman takardun da suka shafi shari'ar da ta shafi mallam Zakzaky.
--
#BAYAN_YA_YANKE_HUKUNCI.
--------
Bayan ya yanke hukuncin cewar,dole ne asaki mallam Zakzaky da matarsa,kuma dole ne abiyasu diyar zunzurutun kudi miliyan hamsin (50,000,000) tare da gina masa gidansa a Zariya ko kuma inda yake son zama a arewacin kasar nan.Ya kuma bada umarnin cewa dole ne asamo wani dan sanda babba yayi masa rakiya ba tare da tursasawa ba da sauransu,sai mai bamu labarin yace 'mun lura sosai cewar,mafi yawan yan Najeriya masu ilimi da hankali da hangen nesa sun yi matkar jin dadin wannan hukuncin tare da jinjinawa shi alkali Kolawole' Yace ya samu sakonnin jinjina da yi masa fatan alheri kuma ya kara samun farin jini a tsakanin abokansa alkalai da lauyoyi.Y samu gayyata zuwa wasu tarukan da zaman bita domin yi masa jinjina da kara masa kwarin gwiwa a kan aikinsa,kuma ya karyata gwamnatin dake cewa wai alkalai basa yin adalci sai cin hanci da karbar rashawa.
--
Yace tun bayan da yabyanke hukunci yabsake lurabda cewa,wadancan jami'an gwamnatin masu kiransa da kawo masa ziyara duk sun janye jikinsu kuma an sake yin wasu bakin fuska masu nuna masa alhinisu da rashin jin dadin hukuncin nasa.

 Yace su kansu yan shi'an nan da ake cewa basa bin dokar kasar nan,sai gashi nan sun zo kotu neman adalcin abinda suke ganin zalinci aka yibmusu.Yace idan muka kibyi musu adalcin muka murda shari'ar ai kamar mun sake nuna musu ne cewar tabbasa babu doka akasar kuma babu adalci akasar.Wannan kuwa ba karamar illa zamu yiwa kasar ba.Sannan zamu fitar da duk wata fata da tunanin samun adalci a kotuna.Yace babban abinda alkali Justice Gebreil Olukolawole yake fata a yanzu shine na ganin cewar ita ma gwamnatin ta cika arkawarin da ta dauka na cewar zata yi mulki mai adalci a kasar wajen sako Ibrahim Zakzaky domin nunawa duniya cewar tabbas ita gwamnati ce mai bin doka da oda kamar yadda take fadawa yan kasa,sannan kuma zata cika arkawarin rantsuwar da suka yi bayan an zabesu,na cewar zasu martaba duk dan kasa ba tare da nuna banbancin bangare ko addini ko kabilarsa.
---------------------
Nasir Isa Ali (Abu Mhammad) Ya Rubuta A Ranar 1-1-2017. Sabuwar Shekarar Miladiya.

#FREEE_ZAKZAKY_DOLE